RAYUWA BATA DA TABBAS 🙆🏻♂️
.
🍁 Mallam rayuwa bata da tabbas, kana cikin tsaka da jin daɗinta zata yanke maka ta rabu dakai, babu ruwanta da ƴaƴa, dukiya, mulki ko sarautarka, da zarar ta ƙetaro gareka to hakika babu abinda zai hanata ɗaukar rayuwarka.
🍁 Kabi a hankali, ka kawar da duk wani jiji da kanka ka dawo kabi Allah, haƙiƙa girman kai babu abinda zai haifar maka face ƙasƙanci a ranar lahira.
🍁 Duk yadda kaso ka kai wani mataki a rayuwa, na mulki ko na sarauta ko kuma na tarin dukiya, Allah mai iya baka sune, amma da zarar rayuwarka ta ƙare, to haƙiƙa babu jinkiri ko ƙarin lokaci a gareka, duk abinda kake dashi ɗin na mulki ko na sarauta ko tarin dukiya, babu wacce zaka tafi dashi cikin ƙabarinka, don haka kayi ƙoƙari kayi amfani da damarka wajen kyautata alaƙarka da Allah, hakan shine abinda zai amfaneka a lahirarka.
SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/DailyHadithss
