MACE MAI DAJARA.
-
"Mace mai ƙimah da daraja ita ce wacce tasan mutuncin kanta, da kuma darajar addinin ta, duk inda taje bata ɓoye siffarta ta musulunci da tarbiyyar da musulunci ya bata, takan wanzar da kamannin musuluncin ta da kuma kalamarsa, bata jin kunyar siturta jikinta a duk inda take, saɓanin waɗanda suke jin kunyar bayyanar da siffar su ta musulunci a gurin waɗanda ba musulmai ba"
-
"Da yawa daga cikin matan mu musulmai, idan suka yi tarayya da waɗanda ba musulmai ba, sai kaga suna jin kunyar bayyanar musu da shigarsu ta musulunci, wannan kuma harda wasu daga cikin mazan ma"
-
"Zaka samu mace a cikin gidan iyayenta tayi shiga ta kamala, amma da zarar taje gurin da za suyi tarayya da waɗanda ba musulmai ba, sai ta sauya yanayin shigar tata ita ma sai ta koma shiga irin ta Arna, musamman ma a manyan makarantunmu na zamani"
-
Telegram channel
https://t.me/hausaislamicpicturesquotes
-
Facebook group
https://www.facebook.com/groups/4329860357034439/?ref=share
