WANDA YA SAUKE AL-QUR'ANI, BAI SAN FASSARAR SHI BA , YAYI LAIFI ?



WANDA YA SAUKE AL-QUR'ANI, BAI SAN FASSARAR SHI BA , YAYI LAIFI ?

*TAMBAYA*❓

Assalamu alaikum. Malam ina da tambaya na sauke Qurani amman ban san fassaransa ba, kuma ina yawan tilawa. To ya matsayin karatun nawa ?

*AMSA*👇

Wa'alaykumussalam To 'yar'uwa karatunki ya yi, mutukar kina yinsa ta tajwidi, ba wajibi ba ne sai kin hada haddar qur'ani da sanin fassarar shi, domin akwai daga cikin sahabbai wadanda fassarar wasu daga cikin ayoyin da suka haddace ta shigewa duhu, amma in hakan ta samu zai fi kyau, saboda hakan ita ce hanyar wasu daga cikin sahabban Annabi s.a.w, An rawaito wasu daga cikin magabata sun haddace qur'ani tun suna shekaru bakwai da haihuwa, zai yi wuya ace hade da fassarar suka haddace a irin wannan shekarun. Sayyadina Umar ya karanta Aya a suratul A'amah a cikin hudubarsa an tambaye shi fassararta bai sani ba, hakan sai ya nuna yin hakan ba wajibi ba ne, amma kuma shi ne ya fi. 

Allah Ne mafi sani.

 *Dr, Jamilu Zarewa*

Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)