WANDA YAKE CIWON IDO, ALWALA ZA TA FADI A KANSA?



WANDA YAKE CIWON IDO, ALWALA ZA TA FADI A KANSA?

*TAMBAYA*❓

Assalamu Alaikum, Mallam Ina da tambaya? Idan mutum aka yi masa aiki a ido an ce kada ruwa ya taba, to, idan zai yi sallah Taimama zai yi ko zai iya yin alwala ba tare da sa ruwa a wajen ba? Allah ya saka da alkhairi. 

*AMSA*👇

Wa Alaikum Assalam, Zai yi alwala cikakkiya, sai ya tsallake wurin da yake da ciwon, saboda Ka’idar :
 ﺍﻟﻤﻴﺴﻮﺭ ﻻ ﻳﺴﻘﻂ ﺑﺎﻟﻤﻌﺴﻮﺭ 
Duk ibadar da za a iya yin wani bangarenta, to, dukkanta ba ya saraya, saboda rashin iya aikata wani bangarenta, sai fa idan bangaren na ta, shari’a ba ta bukatarsa, kamar mai olsar da zai iya yin azumi zuwa Azahar ya sare. 

Allah ne mafi sani 

 *Dr. Jamilu Zarewa*

Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)