IDAN KA SAKI MATARKA, BAN YAFE MAKA BA



IDAN KA SAKI MATARKA, BAN YAFE MAKA BA.
:
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikum.
Idan uba yace wa Dan shi kar ya sake matar sa, in ya sake ta bai yafe ba. Toh idan yaron ya sake ta yana da laifi ne a wurin Allah?
Yaron auren dole aka masa da matar, kuma matar ta ki zama a gidan. ba su ma taɓa hada shinfida ba, gashi baban shi ya gargade shi kar ya sake ta ?.
:
*AMSA*👇
:
Wa alaikum assalam, matukar Manufofin zamantakewar ba za su tabbata ba in su ka cigaba da zama tare ya halatta ya sake ta, saboda cigaba da rike ta saɓon Allah ne, biyayya ga Allah tana gaba da biyayya ga Iyaye.

Allah yana cewa a suratul Bakara aya ta (229) "Saki karo biyu ne, bayan haka kuma sai a rike ta da kyautatawa ko kuma a rabu cikin salama", a aya ta (230) Allah ya halattawa mace ta fanshi kanta in ta ga ba za ta iya tsayawa da hakkokin aure ba, Idan suka rabu Allah zai azurta kowa daga falalarsa kamar yadda ya zo a Suratun Nisa'i .

Daga cikin Manufofin aure akwai samun Zuriyya da nutsuwa da kuma debe-kewa, rintse ido daga kallon Haram, mutukar Manufofin suka goce saki yana halatta.
Ba duk mummunar addu'ar iyaye Allah yake amsawa ba, in da Allah yana amsa duka munanan addu'o'in mutane da sun mutu Miris, kamar yadda Allah ya yi bayani a Suratu Yunus aya ta (11).

Allah ne mafi sani

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
Post a Comment (0)