ANNABI DA SAHABBANSA // 091



ANNABI DA SAHABBANSA // 091
.
Mawallafi: Baban Manar Alqasim
.
YAQIN KHANDAQ/ AHZAAB
Bayan tsoratar da Makkawa suka yi wanda ya sa suka koma gida ba shiri an sami kusan shekara cur ba tare da wata matsala ba, don dama Quraishawa ne ke kawo matsala daga waje, yanzu tsoro ya shige su, ba su da wani katabus, har Yahudawan da ke ciki sun yi la'asar, tun daga Banu Qainuqaa zuwa Banu Nadeer, duk an kore su daga Madina saboda butun-butun din da kullum suke yi wa musulmai, sai dai Banu Nadeer har da haka ba su daddara ba, don sam ba su koyi darasi ba, nasarar da musulmai suka samu a 'yan tsakankanin ma dada tago su ta yi har suka fara sabon shirin da suke ganin kwab daya za su yi wa musulmai su gama da su, daga nan kuma ba wani abu da za a sake kiran sa da sunan muslunci.
.
Da yake bisa al'adarsu ba za su iya fitowa gaba da gaba a kara da su ba sai suka zabo mutum 20 daga cikin manyansu na Banu Nadeer da shugabanninsu, suka tura su Makka inda za su gana da Quraishawa, a can ne za su tunzuro su, kuma su nuna musu cewar za su taimaka musu zuma ko madaci, dama can ba wani abu ya sa Quraishawa suka yi rauni ba tsoro ne, don haka nan take za su karbi tayin da suka yi musu, ilai kuwa.
.
Su Quraishawa gani suke wannan taimaka musu za a yi wajen kawar da musulmai, don ko ba don daukar fansar kashe manyansu ba akwai zancen kasuwancinsu da shi ne babban abin da yake ci musu tuwo a qwarya, bare kuma ga zancen jini da suke ba wa mahimmanci sama da komai, dama ta samu da za su dawo da sunansu da ya gama balbalcewa a idon sauran Larabawan, bayan wannan qullin da Yahudawan suka yi a Makka sai suka wuce zuwa Gatfan suka janyo hankulansu kamar yadda suka yi a Makka su ma suka amsa.
.
Da haka ne siyasar Yahudawa ta sami nasara inda suka hada kan mushrikai a wuri guda, qabilu ne masu dama qarqashin wadannan wurare guda biyu, an sami mutum 4,000 da suka fito daga qabilun Kudanci wato Quraishawa, Kinana da wadanda suke da qawance da su irin su mutanen Tuhaama duk suka fito qarqashin jagorancin Abu-Sufyan RA (da wannan za mu gane cewa qarya ake yi wa zuriyar yadda ake sifanta ta da ragonci, ba shakka ko tun gabanin muslunci Abu-Sufyan RA yana kan gaba, kamar yadda ya kasance a wajen ba wa Annabi SAW kariya a yaqin Hunain lokacin da abu ya yi qamari).
.
Haka dai sojojin suka je suka hadu da na Banu Saleem, ta bangaren Gabashi kuma aka sami qabilolin Gatfaan: Wato Banu Fazaara wanda Uyaina bn Hisin yake jagoranta, sai kuma Banu Murra qarqashin jagorancin Harith bn Auf, sai Banu Ashjaa da Mas'ar bn Rukhaila yake shugabanci, a gefe kuma ga Banu Asad da sauransu, duk suka fuskanci Madina bayan sun gama daidaita komai a tsakaninsu, sun isa jikin ganuwar Madina a lokacin da adadinsu ya kai mutum 10,000, ka ga mayaqan da muslunci ya tara mafi girma shi ne wanda ya fito zuwa Badar na biyu, wato rundunar da ke dauke da sojoji 1,500.
.
In ka dubi yawan sojojin da suka taru don yaqar musulman da ke Madina sai ka ga ba ma musulman ba in aka hada kowa da kowa ciki har da mata tsahhi da qananan yara sam ba su kai yawan maharan ba, da a ce wadannan rundunonin sun iya fado wa musulmai ba zato ba tsammani, da sai dai kuma abin da Allah SW ya tsara zai wakana, don ba yadda za a iya sifanta yadda yaqin zai kasance, sai dai kamar yadda muka dauko tarihin tun farko Annabi SAW bai taba yarda ya yi zaman dirshan ba, ya baza 'yan leqen asiri a tsakiyar abokan gaba, suna fara yin wannan shirin labarin ya iske shi har Madina.
.
Nan take Annabi SAW ya kira wani taro na gaggawa wanda manyan hafsoshin sojin muslunci suka halarta, aka fara tattauna yadda za a ba wa qasar muslunci kariyar da take buqata, bayan doguwar tattaunawa a qarshe suka tsaya a kan shawarar da babban sahabinnan wato Salmanul Farisiy RA ya bayar, mutumin tsohuwar qasar Iran ne, da yawanmu sun san cewa dadaddiyar qasar kafurci ce mai qarfin gaske a duniya, ta sha gwagwarmaya da Rumawa, har sun riqa yin musayar nasara, shi ne ya ba da shawarar a gina Khandag.
.
Shi Khandaq wani wawukeken rami ne da zai kewaye gari gaba daya, ta yadda ba wanda zai shiga garin sai ya shiga ramin, qasar ramin sai a turo shi bangaren gari, ba shakka wannan shawara wata sabuwar mafita ce wace Larabawa ba su san da ita ba a lokacin, nan da nan Annabi SAW ya sa aka yi gaggawar zartar da wannan mihimmiyar shawarar, ta yadda aka dora nauyin haqa zira'i 40 a kan duk mutum goma, suka kama aikin gadan-gadan ba sassautawa, Annabi SAW yana jinjina musu don qara musu qwarin gwiwa.

Rubutawa:- Babban Manar Alqasim 
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)