KASHEDINKU DA SHIGA GIDAJEN MATA❌
Manzon Allah (SAW) ya ce: "Kashedinku da shiga (gidajen) matan aure, sai wani mutum daga cikin mutanen madina ya ce: Yaa Manzon Allah ba ni labari dan uwan miji(kanin miji/yaya) fa? Ya ce; Kanin miji mutuwa kenan!(Ma'ana ai shi a ka fi tsoro da tsammanin fitina daga gareshi". Bukhary
Malamai sun ta fi a kan cewa: Al-Ahmaa'u(hamw): Su ne makusantar miji ko makusantan matar maza, kaman babanshi, baffansa, dan uwanshi(yaya ko kani) da dan dan uwansa, ko dan baffansa, ba ya halatta su ke shiga gidajen mata yadda suka ga dama da kebanta dasu.".
KUMA BABU WANI ABU MAI SUNA: WASAN KANIN MIJI A MUSULUMCI!!!
________________
"Cewa makusancin miji(kani ko yaya ko dan uwa) mutuwa ne, Ma'ana: Shi a ka fi tsoro a kansa ma sama da waninsa, kuma an fi tsammanin sharri da fitina daga gurinsa saboda samun damarshi na shiga ga matar da kebanta da ita ba tare da wani ya yi masa inkari ba, sabanin idan wani bare ne. Al'adar mutane a wannan bangaren shine yin sakaci da wannan(bangaren) sai ka ga kanin miji ko dan uwan miji ya rika kebanta da matar dan uwansa! Wannan shine mutuwar! Don haka shi ya fi kusa da a hanashi sama da bare!(duk da dukansu haramun ne).
النووي في شرح مسلم
#Zaurandalibanilimi
TELEGRAM
https://t.me/Zaurandalibanilimi