TUN A DUNIYA KE NAN!



TUN A DUNIYA KE NAN!

Ɗaya daga cikin manya-manyan shugabannin "Magol" ya karɓi addinin kiristanci, aka shirya biki domin karrama shi.

A wurin bikin, wani malamin Kirista ya gabatar d jawabinsa wanda a ciki yake IZGILI da kuma zagin Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallama). A dai-dai lokacin da yake furta kalaman ɓatancin sai wani kare dake ɗaure a gefe ya farma masa da yakushi da cizo, da ƙyar mutanen wurin suka ƙwace shi bayan karen yaji masa mummunan rauni.

Wasu daga cikin mahalatta taron suka ce masa: "wannan ya faru da kai ne sakamakon kalaman É“atanci da ka yi ga Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallama)". 

Sai ya ce: "Lokacin da nake jawabi, na kasance ina nuna karen da yatsana, sai ya fusata yana tsammanin dukansa nake son yi, shi yasa ya farmini".

Ya ci gaba da bayanansa akan MA'AIKI (Sallallahu Alaihi Wasallama), kafin kammala jawabinsa karen ya sake afka masa a karo na biyu, ya damÆ™i wuyansa. A haka wannan malamin kiristan ya faÉ—i matacce a wurin taron. 

Wannan ya sanya mutum 40,000 daga mabiya"MAGOL" suka rungumi addinin Musulunci.
 [إمام الذهبي/معجم الشيوخ]
Post a Comment (0)