KADA KASA RAZANA DA FIRGICI A ZUKATAN MUTANE YI KOKARI KASA MUSU FARINCIKI.
Wani dattijo malami suna tafiya da daya acikin dalibansa a tsakanin gonaki, sai suka ga wasu tsofaffin takalmi agefen wata gona wanda suka tabvatar na daya daga cikin ma'aikatan gonan ne daya aje zai waiwayesu bayan yagama aiki.
Sai dalibin yace, me kagani ya malamina in boye takalmin wannan mutumin inga inya fito yazaiyi? Sai malamin yace, a'a Sam bai kamata mujiyar dakammu dadi da shiga bakincikin wasunmu ba zaifi kyau tunda kai mai wadata ne kasanya kudi acikin kowane daya acikin takalmin sai mugani inyazo sawa yazai yi.
Sai dalibin ya amince da shawaran malaminsa yasaka kudi acikin takalmin, sannan suka buya akusa da wurin.
Bayan wani ma'aikaci ya fito kayan jikinsa ajike saboda tsananin wahalar aiki sai yasaka takalmi daya yaji yaji wani Abu aciki, sai yatsaya yafito dashi sai yaga kudi ne yacika da mamaki, yakara saka dayan kafan a dayan takalmin sai yaji Abu 'iri daya namma yaciro yaga irin kudin da yagani ana farko sai jikinsa yayi sanyi yayita kallon wannan kudi yakara murje idonsa dondai ya tabbatar ba mafarki yakeyi ba. Sannan yaduba gefensa baiga kowa awurin ba.
Sai wannan ma'aikaci yahada kudinnan duka yasanya a aljihunsa yafadi akan gwuiwoyinsa yadaga hannayensa sama da madaukakiyar murya yace, na gode maka Allah wanda yasan cewa matata bata da lafiya kuma yayana suna jin yunwa basu da abinda zasu ci ya tseratar dani da 'ya'yana daga halaka, sannan ya dade a tsugune akan cinyoyinsa yana godiya ga Allah yana jinjina ga sarki mai tausayi da jinkai.
Sai dalibin wannan malamin ya tasirantu da yanayin wannan mutum a zuciyarsa sai idanuwansa suka fara zubar da kwalla. Sai malaminsa yace hakan baifi ba akan tunaninka na farko na cewa aboye takalmin fakirin!?
Sai dalibin yace haqiqa nakoyi darussa wanda bazan manta dashiba matukar ina rayuwa!!
Darussan kuwa sune.......lokacin da kake badawa zakafi jin dadi da dacewa fiye da ace Kaine kake karba.
Sai malaminsa yace mai kasani ya Dana, ita kanta bayarwa ko kyauta nau'i nau'i CE.
Afuwa alhalin kana da 'ikon daukan fansa kyauta CE.
Yima dan'uwanka addu'a ba tareda saninsa ba kyauta CE.
Karbar uzurinsa da yaye mummunan zato daga garesa kyauta CE.
Kauda kai daga shiga cikin mutuncin dan'uwanka ko yimasa giba kyauta CE.
Ya Allah kasa mudace duniya tareda ranar lahira da zamu tsayu agaba gareka.