HUKUNCIN WANDA YAJE WURIN ƊAN DUBA KO BOKA
Daga Safiyyah bntu Abi Uzaid daga Daya daga cikin Matan Manzon Allah ﷺ ورضي الله عنهن daga Manzon Allah ﷺ yace:
(Wanda yaje wajan malamin duba ko Boka,sannan ya tambayesa wani abu kuma ya gaskatsa akansa,baza’a karbi sallolinsa ba na kwana arba’in)
@رواه مسلم.
Awata riwayar yana cewa;
(Duk wanda yaje wajan mai yin duba ko Boka,kuma ya gaskata abinda ya fada masa,hakika ya kafircewa abinda aka saukarwa da Manzon Allah SAW)
@وفي مسند الإمام أحمد ،وأبو دَاوُدَ والحاكم والذهبي والألباني والترمذي وابن ماجه وغيرهم :
Daga daya daga cikin Matan Manzon Allah ﷺ tace;Manzon Allah ﷺ yace;
(Wanda yaje wajan malamin duba sai ya tambaye shi wani abu,baza’a karbi sallarsa ba ta kwana arba’in)
@أخرجه مسلم[2230].
Allah ne mafi sani
Allah ka karemu da imanin mu baki daya.