AHIR ƊINKA DA KWANCIYA RUB-DA-CIKI LOKACIN BACCI
Kwanciya Rub-Da-Ciki Itace Kwanciyar Da Ake Kwantawa Akan Ciki Fuska Na Kallon Ƙasa, Yayin da Bayan Mutum Ke Kallon Sama. Wannan Kwanciya Haramun Ce a Musulunce Saboda Hani da Manzon Allah (ﷺ) Yayi Game da Ita. Hadisi Ya Tabbata Daga Abi-Hurairah (ra) Yana Cewa:
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِي اللّهُ عَنهُ قَالَ: رَأَى رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ رَجُلًا مُضْطَجِعًا عَلَى بَطْنِهِ فَقَالَ: {إِنَّ هَذِهِ ضِجْعَةٌ لَا يُحِبُّهَا اللَّهُ}
(رواه الترمذي)
An Karɓo Daga Abi-Hurairah (ra) Yace: Lallai Manzon Allah (ﷺ) Yaga Wani Mutum Kwance Akan Cikinsa, Sai Yace Dashi: “Lallai Wannan Kwanciya Ce Da Allah Baya Sonta”.
(Tirmizi Ya Ruwaitoshi)
Duk Lokacin da Mutum Zai Kwanta Bacci Bashi da Tabbacin Ubangiji Zai Dawo Masa da Ransa Ya Cigaba da Rayuwa. Ya Kai Ɗan Uwa Shin Zakaso Ubangiji Ya Amshi Ranka Kana Cikin Yin Abinda Bayaso?
Idan Bazakaso Hakan Ba, To Ka Kiyayi Kwanciya Rub-Da-Ciki Yayin da Zakayi Bacci Domin a Cikin Baccin Allah Yana Iya Amsan Abinsa.
Har Ila Yau Hadisi Ya Tabbata Daga Abi-Zarrin (ra) Game da Hani Akan Wannan Kwanciya.
عَنْ أَبِي ذَرٍّ قَالَ رَضِي اللّهُ عَنهُ فَال: مَرَّ بِيَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَأَنَا مُضْطَجِعٌ عَلَى بَطْنِي، فَرَكَضَنِي بِرِجْلِهِ وَقَالَ: (إِنَّمَا هَذِهِ ضِجْعَةُ أَهْلِ النَّارِ)
(رواه إبن ماجه)
An Karɓo Daga Abi-Zarrin (ra) Yace: Manzon Allah (ﷺ) Ya Wuceni Ina Kwance Akan Cikina, Sai Ya Shureni Da Ƙafarsa Sannan Yace: “Wannan Kwanciya Ce Ta Ƴan Wuta”.
(Ibn Majah Ya Ruwaitoshi)
ALLAH KA AZURTAMU DA MUTUWA MUNA MASU AIKATA ABINDA KAKESO BA WANDA BAKASO BA
✍🏽Abu Aysha Al-Maliky