HUNKUNCIN SAUKEWA MAMACI ALQUR'ANI BAYAN YA MUTU
TAMBAYA❓
Assalamu alaikum Wai Malam Meye Hukuncin Saukewa Mamaci Al-qur'ani?
AMSA👇
Wa'alaikum assalam. To malamai sun yi sabani akan wannan mas'ala zuwa maganganu guda uku:
1. Bai halatta ba, saboda ba'a samu wani nassi da yake nuni zuwa haka ba, kuma ita ibada ba'a yinta sai da nassi na musamman, sannan kuma mutum ba shi da wani abu sai aikinsa, kamar yadda aya ta 39 da take cikin suratu Najm, take nuni zuwa haka, tun da ba'a samu ba, yin hakan zai zama bidi'a, wannan ita ce maganar farko ta Shafi'i.
2. Ya halatta ayi, saboda hadisan da suke nuna cewa mamacin yana iya amfana da abin da mai rai zai masa, kamar hadisan da suka yi umarni da yi masa sallah da nema masa gafara bayan ya mutu, da yi masa sadaka, wannan shi ne maganar mafi yawan malamai, har wasu marubuta ma sun hakaito ijma'i akan haka, saboda mutane sun jima suna yi kuma malamai ba su yi musu inkari ba.
3. Akwai wadanda suka tafi akan cewa: idan dansa na cikinsa ya yi masa, to ladan zai same shi, amma wanda ba dansa ba, ba zai yi masa ba, saboda fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi" Dan mutum yana daga cikin aikinsa" Abudawud ya rawaito shi kuma albani ya inganta shi a sahihu sunani-abi-dawud hadisi mai lamba ta: 2528.
Saidai wasu malaman, suna rinjayar da magana ta uku, saboda fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: "Idan dan'adam ya rasu ayyukansa sukan yanke sai dayan abubuwa guda uku: sadaka mai gudana, ko ilimin da ake amfana da shi, ko ɗa nagari da yake masa addu'a" kamar yadda Tirmizi ya rawaito shi kuma ya inganta shi a hadisi mai lamba ta: 1376.
Wadancan hadisan kuwa da masu Magana ta biyu suka kafa hujja da su, to za'a yi amfani da su ne a iya inda suka zo, amma ba za'a yi kiyasin karatun qur'ani akan su ba.
Don neman Karin bayani: duba majmu'ul fataawa: 24\366 da Nailul Audaar 4\112 da Ahakamul jana'iz shafi na: 171.
Allah shine mafi sani.
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.