ME YASA BAZA MU ZAMA MASU HAKURI DA YAFIYA BA?
Shin Dan Uwa baka sani bane cewa YIN HAKURI IBADA BANE?
Shin dan uwa baka sani bane cewa HAKURI dabi'ace daga cikin dabi'un fiyayyen Halitta bane? Kokuwa bada shi kake koyi bane?
Shin baka san irin lada da sakamakon da masu hakuri suke samu bane? Kokuwa baka muradin kyakykyawar makomane?
TO KA SAURARA KAJI.
Acikin suratul Al-IMRANA Allah madaukakin Sarki yana cewa: YAKU WADANDA KUKA YI IMANI KUYI HAKURI,KU JURE.......Har zuwa karshen ayar yake cewa...KUJI TSORON ALLAH KO KWA SAMU BABBAN RABO.
Acikin suratul ZUMAR kuma:
ﻗﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ : ﺇﻧﻤﺎ ﻳﻮﻓﻰ ﺍﻟﺼﺎﺑﺮﻭﻥ ﺃﺟﺮﻫﻢ ﺑﻐﻴﺮ ﺣﺴﺎﺏ . ( ﺻﻮﺭﺓ ﺍﻟﺰﻣﺮ ).
Allah madaukakin sarki ya ce: KADAI MASU HAKURI AKE CIKAWA LADANSU BATARE DA KIDANƳAWA BA.
Dan uwa ka sani cewa Allah yana saukar mana da abubuwa da yawa na fitintunun rayuwa,Don ya jarraba mu ya nuna waye yafi wani kyakykyawan Aiki kamar yadda ya fada cikin suratul Mulk aya ta 2.
Don haka Dukkan kunci ko tawayar dukiya ko wani abun tashin hankali da ya same ka kayi Hakuri,Allah yana cewa dukkan tsanani yana tare da sauki.
Baka san abunda Allah ya nufi ko ya tanadar maka dalilin hakurin naka ba,Ta yiwu Dalilin hakurin da kayi Allah Ya musanya maka abunda ka rasa da mafificinsa.
Yin hakuri kyakyakyawar dabi'a ce daga cikin dabi'un Ma'aiki S.A.W Mas'ud R.A Ya ce: Ni ina ganin cewa kamar Manzon Allah S.a.w yana kwaikwayon wani Annabi ne daga Annabawa A.S Da mutanensa suka buge shi,suka ji masa rauni,sai yake shafe jinin daga fuskarsa yake cewa: YA UBANGIJI KAYI GAFARA GA MUTANENA SU BASU SANI BANE.
Kaji fa yadda aka jiwa Manzon Allah S.A.W rauni har jini yana zuba a fuskarsa batare da ya aikata laifin komai ba amma yayi Hakuri har ya daga hannu yana nema mawa wadanda sukayi masa wannan aika-aikan gafara.
Inda nine ko kai aka yi mana wani abu makamancin wannan da abunda zai fara zuwa zuciyarmu shine tunanin daukar fansa ko?
To kada muyi haka don acikin suratul Anfal Allah yana cewa KU NEMI TAIMAKO AKAN YIN HAKURI DA SALLAH,LALLE ALLAH YANA TARE DA MASU HAKURI.
To tunda mun ji cewa Allah yana tare da masu hakuri me zai hana ba zamu kasance tare da Allah ba ? Kokuwa akwai wata riba da mutum zai samu cikin rashin hakuri? Hausawa ma sunyi wata karin magana cewa ME HAKURI SHI YAKAN FADA DUTSI HAR YASHA ROMONSA Kaga idan ka fahimci Hausar zaka ga ana nufin cewa Me HAKURI Shine da Nasara.
Mun samu a Hadith Qudsi Allah yana cewa (KUDABI'ANTU DA IRIN SIFFATA,NINE ME HAKURI)
ALLAH kenan da kansa yake cewa mu dabi'antu da irin siffarsa MA'ANA ASSABUR me Hakuri Manzon Allah S.a.w ya bamu Maganin da zai rage ko ya kawar mana da musiba idan ta same mu aciki akwai yin Hakuri Har yake cewa Musulmi su dinga yin hakuri da musifar da ta same su da tuna masifar rabuwa da Ni".
ALLAH YA SANYA MU DAGA CIKIN BAYINSA MASU HAKURI,YA GAFARTA MIN CIKIN ABUNDA NAYI KUSKURE.
Zurmi