KIRAN SALLAH MA WAHAYIN SHI AKA YI ?



KIRAN SALLAH MA WAHAYIN SHI AKA YI ?:
:
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikum 
Malam, kira sallah (adhan) Allah ya saukar da shi kaman yan da YA saukar da Al Qur’ani zuwa ga Annabi Mohammad (S.A.W)? Ko kuma ya aka samota acikin addini muslinci?

:
*AMSA*👇
:
Wa’alaykumussalam, 

Hadisi ya inganta cikin swahihul bukhari 569 daga Nafi’u cewa ibn Umar yace lokacin da musulmai suka zo garin madina sukan taru su rika kirtatan lokacin sallah ba’a kiran sallah, wata rana sai suka tattauna wasu sukace a samu kararrawa irin kararrawar nasara, wasu sukace a’ah, a samu kaho ko wusir irin na Yahudawa sai umar yace ku fara aika wani yayi kiran sallah, sai manzon S. A. W yace ya kai bilal tashi ka kira sallah.
Akwai ruwayar data zo cikin sunan na abi dauda 420, wadda ta nuna cewa  Abdullahi bn zaid ibn Abdi rabbihi wata rana yana tsakanin bacci da falke sai wani yazo masa ya koya masa kiran sallah, da gari ya waye yazo wajen manzon Allah ya bayya masa, Ashe Umar bin khaddab ya dade da yin mafarki kiran sallah kusan kwana ashirin amma bai gaya wa manzon Allah ba sai ranar da Abdullahi ya gaya wa manzon Allah, sai manzon Allah bai ce umar me yasa baka gaya mun tun tunni ba. sai yace ya kai bilal tashi kaje ka kira sallah.

Wannan shine tarihin samuwar kiran sallah.

Wallahu a’alam. 

Malam *Nuruddeen Muhammad (Mujaheed)*

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)