YA HALATTA AMARYA DA ANGO SU SANYA ZOBEN ZINARI A RANAR AURENSU?:
:
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikum
Dan ya halatta Amarya da Ango su sanya zoben zinari a ranar aurensu?:“`
:
*AMSA*👇
:
وعليكم السلام ورحمة الله.
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ
Haramun ne ga Namiji yasa zobe ko wani abu na zinari a kowanne irin yanayi.
_*Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam)* ya haramta zinare ga mazan wannan al’umma. Yaga wani mutum yana sanye da Zobe na zinare sai shi *(Manzon Allah)* ya cire zoben daga hannunsa (mutumin) sannan yace: *Shin dayanku zai dauki garwashi daga wuta ya rike a hannunsa*_
_*(Muslim ya ruwaito shi, Al-Libaas wal-Zeenah , 3897).*_
Saboda haka bai halatta ga Namiji yasa Zoben zinari. Amma idan zoben azurfa ne ko sanholama ko wani karfe mai kyalkyali babu laifi Namiji zai iya sanyawa a hannunsa.
Amma ya halatta ga mata suyi amfani da Zoben zinare da kayan da akayi su da zinare.
Saka Zobe tsakanin amarya da ango ko tsakanin Mata da Miji ko tsakanin masoya masu niyyar yin aure, idan an sashi ne da sunan zai kara karfafa soyayyar junansu. To wannan haramun ne qada’an!!!. Saboda ya zama wani nau’in ne na shirka.
_*(Al-Fataawa al-Jaami’ah lil-Mar’ah al–Muslimah , Mujalladi na 3, shafi na 914-915)*_
والله أعلم،
Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇
https://wa.me/+2348087788208
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ