NA GODE TAWAN
♡
Samun ki a rayuwata ya bani
k'warin guiwar tunkarar
matsalata da samun nasara a kan
dukkan abun da na sa a gaba.
Kulawarki a kaina na k'ara min
jarumta, soyayyarki a gare ni na
sanyawa na ji ni a matsayin
cikakken mutum. Na gode
masoyiyata, ina alfahari da samun ki
a rayuwata. Ina nan cike da
kewarki cikin zumuÉ—in son
Zuwa gareki na sanya ki a
idanuwana.
♡
FATANA DA BURINA
♡
A gare ki nake samun bargo, a
dukkan lokacin da sanyi ya rufe
ni. Ina samun tsaro, a dukkan
lokacin da hatsari ya tinkaro ni.
Ina samun farin-ciki, a dukkan lokacin da damuwa ta lilliɓe ni.
Fatana da burina mu mutu tare mu tashi tare mu rayu tare a gidan Aljanna. Ina Son Ki Aminatu Fiye Da Yadda Nake Son Kaina.
Comr Haidar Hasheem Kano ✍️