ALLAH MADAUKAKIN SARKI YANA DA MAFITA GAMEDA DUKKANIN WATA MATSALAR DA TAKE DAMUNKA!

ALLAH MADAUKAKIN SARKI YANA DA MAFITA GAMEDA DUKKANIN WATA MATSALAR DA TAKE DAMUNKA!




"Koda yaushe muna yin tunani ne akan yawan matsalolin da suke damun mu ne a rayuwa, muna mantawa da cewa lallai fa haƙiƙa Allah yana da mafita daga dukkanin kowace irin matsalar da ta dame mu a rayuwa"

"A rayuwa idan muka fuskanci Allah maɗaukakin sarki, muka koma gareshi da tuba cikin nadama da ƙas-ƙantar da kai, haƙiƙa Allah zai saurare mu, zai kuma yaye mana dukkanin damuwa da take damun mu ko ba-daɗe ko ba-jima"

 "Musamman idan munyi haÆ™uri mun kuma doge akan biyayya ga Allah ta'ala"

"Muji tsoron Allah, sai Allah ya warware mana damuwar mu, mu kauce ma saɓonsa, sai yaji ƙanmu, kada mu bari shaiɗan yayi tasiri akanmu ya shiga tsakanin mu da ubangijin mu Allah ya kuma halaka mu ƙarshe mu zamto ababen yin nadama a ranar ƙiyamah"


Yããã Allah kasa Mudace Duniya Da Lahira


Post a Comment (0)