KHUƊUBAR MASJIDIS SALAFIYYA BIU BORNO STATE: 19/SHA'ABAN/1442-HJRY 02/APRIL/2021-MLDY




KHUƊUBAR MASJIDIS SALAFIYYA BIU BORNO STATE:
19/SHA'ABAN/1442-HJRY
02/APRIL/2021-MLDY


GABATARWA:--- Abubakar BN Mustafa Biu 

♦️TOPIC👉🏼 [[ ƘARAMIN YARO YAJA MAHAIFINSA MASALLACI]] 

➖MUQADDIMA✔️
  Yaku bayin ALLAH! mu bautawa ALLAH SW mudaina tukuna, dominfs ibada shine kariya kaɗai daga azabar ALLAH, 
💡ALLAH SW yace <<ya waɗanda sukayi imani kukare kawunanku da iyalanku daga wutanda makamashinta mutanene da duwatsu...... >> {SRT TAHRIM-6}

➖ƘISSAR YARONDA YAZAMA SANADIN SHIRIYAN GIDANSU✔️
  Wannan ƙissar SHEIKH IBRAHIM AL-FARIS ya kawo cikin littafinsa
 [قصص معبرة للأطفال]
YACE wannan ƙissar da gaskene kuma an yaɗata a kafofin yaɗa labarai= ƙaramin yarone ɗan aji 3 a primary, Malamansa da matasan Makarantar suna kwaɗaitar dasu ibada da kuma salloli a jam'i (Masallaci) musammanma sallar asuba, tarbiyyannan yayi tasiri ga yaron, amma kash! Wa zai riƙa tayar dashi❓Babansa❓Mamarsa a'a, baswa tashiwa don sallar asuba,
  Yaron ya yanke wata shawara mai haɗari, shine zai hana idonsa barci har asuba, haka yayi, yana jin ƙiran sallar asuba yafito yabuɗe ƙofa, yacika da firgici da tsoro yayinda yaga duhu kuma titinsu tsit ba kowa, kwatsam yaji takun tafiya ƙasa ƙasa, dattijone ke tafiya a hankali tokare da sandarsa tafin ƙafarsa baya taɓa ƙasa sosai, yaron yadubeshi sai yaganeshi ashe kakan abokinsane Ahmad, yabi bayan dattijon da sanɗa ba tareda yasaniba har masallaci sukayi salla haka yabiyoshi da sanɗan har gida yashiga gida yakulle yakwanta yataɓa barci yatashi yatafi makaranta, haka yacigaba a kullum har tsawon zamani, ba wanda yagane a gidansu saidai suna ganin yana yawan barcin rana,
  Kwatsam! Yaro yaji labarin mutuwar yayita kuka mai tsanani na tashin hankali don rasa damar zuwa masallaci don asuba, Hankalin mahaifinsa ya tashi ƙwarai, harma yake cewa= ya kake kukan mutuwar bare, shifa ba babanka bane ba mamarkaba ba ɗan uwankaba, sai ƙaramon yaron yace= kaiconka baba da kai kamutu yafi mini sauƙin baƙin ciki akan mutuwar dattijonnan!
  Hankalin baban ƙaramin yaronnan ya tashi sosai don furucin yaronsa, ya matsa masa da tambayan dalili, sai yaron yace= dattijonnan ina bin bayansa ba da saninsaba ina zuwa asuba...... yakwashe labari kaf yabasu, nan take iyayensa suka fashe da kuka, babannasa hawaye yana shaƙeshi kamar ransa zai fita, haƙiƙa wannan lamarin yayi tasiri a rayuwarsu, yacanza rayuwarsu yazama silar shiriyarsu, daga wannan ranan baban zai tashesu sutafi masallaci suyi sallar asuba, gidan yazanto salihin gida ALHAMDULILLAH, 

➖DAGA DARUSSAR ƘISSAR

 Sakacin iyaye a addini da rashin kamun kansu yana damun 'ya'yansu

 Nagartattun Makarantu da Malamai da abokai suna tasiri matuƙa don gyaran tarbiyya

 Ɗa nagari babban arziƙine ga iyayensa a rayuwarsu da mutuwarsu

 lura da yanayin yara- na daga mafi girman haƙƙin yaran akan iyayensu

 lura da shige da ficen yara musammanma cikin dare

 Yaro da Mahaifinsa kowannensu na iya shiryuwa da ɗan uwansa

➖RUFEWA
  Bayin ALLAH, muyi tanadi domin RAMADAN ya kusanto, kwanaki 10 kacal suka rage, mu fuskanceta da treatment na cututtukanda ka iya hanamu azumi, mu fuskanceta da kyakkyawar ƙudurin rayata da ibadoji, in mun iso da rai sai muyi, in mun mutu kuma musami ladan niyya, 
  Kuma muna jan hankalin uwaye mata masu zuwa jinya asibiti suguji zama babu sutura ta musulunci watama ba riga a ɗakin jiyya, susanifa asibitin ba ɗakinsu bane, ai koda ɗakinkine ba muharraminkiba zai shigo wajibine kirufe jikinki, ballantana asibiti wanda samada maza 100 zasu shigo dubiya, su ma maza suji tsoron ALLAH wajen shiga ɗakin jiyyar mata a asibiti donfa ba matansune kaɗai a ɗakinba, kada su shiga saida buƙatar shigowan kuma su runtse idanunsu kuma suyi saurin ficewa in sun kammala, 

ALLAH YASA MU WANYE LAFIYA- iyayenmu da 'ya'yanmu
AMIN 

viaAbubakar BN Mustafa Biu👇👇

Post a Comment (0)