YA HALATTA NA SAYI KARE SABODA GADI A GIDANA ?
TAMBAYA❓
:
Assalamu alaikum. Dr. Menene hukuncin ajiye kare a gida saboda gadi? Allah muke roko ya karawa Dr lafiya da basira Ameen.
:
AMSA👇
:
Wa alaikum assalam, Ya tabbata a hadisin Bukhari da Muslim cewa: "Mala'iku ba sa shiga gidan da yake akwai hoto ko KARE a ciki.
A wani hadisin mai lamba ta: 2974 da Muslim ya rawaito Annabi s.a.w. yana cewa: "Duk Wanda ya rike KARE, in ba Karen noma ba ko farauta ko kiwo, to Allah zai tauye masa manyan lada guda biyu a kowacce rana.
Da yawa daga cikin malamai sun yi kiyasin KAREN GADI akan wadancan nau'ukan guda uku da suka gabata, don haka ya halatta musulmi ya riki Kare saboda gadi in har akwai bukatar hakan.
Ba ya halatta a siyar da kare kowanne iri ne, saboda Annabi S.a.w ya hana cin kuɗin Kare a hadisin da Muslim ya rawaito kuma ya kira Shi da dauda.
Duk da cewa an halatta wadancan nau'ukan guda hudu saboda bukata saidai bai halatta a siyar da su ba, saboda Ka'ida sananniya a wajan malaman Fiqhu wacce take cewa:
ما جوز للحاجة لا يجوز أخذ العوض عليه
Idan mutun yana bukatar ɗaya daga cikin wadancan nau'uka na karnuka guda huɗu da suke halatta, kuma bai samu wanda zai ba shi kyauta ba, ya halatta ya siya, Amma zunubin sayarwar yana kan wanda ya sayar tun da shi ne bai bayar ba, kamar yadda Ibnu Hazm ya fada a littafinsa na Muhallah 4/793, Ka'ida tabbatacciya a wajan malamai tana cewa:
ما حرم سدا للذريعة يباح للحاجة أو المصلحة الراجحة
Allah ne mafi sani.
Amsawa
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
Yaku Yan'uwa masu Albarka ku taya mu yaɗa wannan karatu/sako zaku samu lada mai yawa, _Amma don girman ALLAH kada ku kwafa ku goge wani abu daga ciki. Kuji tsoron ALLAH