YA SAKI MATARSA SAKI UKU ASHE TANA DA CIKI, SHIN AKWAI SAURAN AURE TSAKANIN SU?
:
TAMBAYA❓
:
Asslm alekum warahmatullah akaramakallah barka da rana ya ayyuka sunana muhd daga sautul sunnah inada tambaya
Nine nasaki matata wata hudu da suka wuce alokacinda nasaketa namata saki 2 lokaci 1 bayantaje gida mukayita zage zage a waya saina kara mata saki 1 bayan wata hudu saita kirani wai tanada ciki. menene makomar aurenmu da ita a shari'a? nagode
:
AMSA👇
:
Wa'alaykumussalam
Aure dai ya kare tunda saki ya kai uku, sai ta jira iddar ta zuwa haihuwa, zaka ci gaba da dawainiya da ita da cikin har zuwa haihuwa daga nan sai ku tattauna yadda shayarwa zata kasance sai ka biya ta shayar maka da yaron ka kamar yadda Alkur'ani yayi umarni.
Wallahu A'alam
Malam Nuruddeen Muhammad (Mujaheed)
Yaku Yan'uwa masu Albarka ku taya mu yaÉ—a wannan karatu/sako zaku samu lada mai yawa, Amma don girman ALLAH kada ku kwafa ku goge wani abu daga ciki. Kuji tsoron ALLAH
Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.