ASIBITIN MAHAUKATA

ASIBITIN MAHAUKATA




A asibitin mahaukata ne, sai wani mahaukaci, mai suna dan-kawu ya tsunduma cikin wani katon tankin ruwa. Da wani mahaukacin, wai shi Sallau ya hangoshi yana neman mutuwa, sai nan take yaje ya tsamo shi. Jin wannan labari sai babban likitan asibitin ya zata lallai Sallau ya warke, kuma ya kamata a yi masa dubawar karshe a sallameshi. likita ya kirashi yace, 'Amma fa Sallau ka birgeni yadda ka tsamo Dan-kawu daga tankin ruwa ka ceci ransa. saboda haka..... kafin likita ya karasa magana, sai ga wani a guje yana cewa: 'ai dan-kawu ya rataye kansa ya mutu'. Jin haka sai Sallau yace,' Kash! Wallahi ba kashe kansa yayi ba. NINE NA RATAYESHI DON YA BUSHE'.....lol inkai ne likitan yaya za kayi?
Post a Comment (0)