HADISIN MU NA YAU📚📿👳🏻♂️⤵️
```Ma aikin Allah s.a.w Yace Babu abinda yake raguwa a cikin dukiya idan anyi sadaka (sai daima ta qaru) Babu abinda yake raguwa ga bawa idan yayi afuwa(yafiya) sai dai qarin girma, Babu Wanda zai kaskantar dakansa saboda Allah face sai Allah ya daukakashi.```
*Muslim ne yaruwaito*📚✍🏻
*NOTE:-👉🏻* _Duk sanda Mutum yabada sadaka kada yayi tinanin dukiyarsa taragu, a'a, tana nan sai dai taqaru, domin kabayar ne akaimaka ita lahira, Wanda idan batanan ba... tayiwu sai dai kaci ka kasayar, haka duk sanda wani yayimaka kuskure Dan kayimasa afuwa🤝🏻 baka fadiba, Kuma baka raguba, illah daraja da Allah zai qara maka, Kuma ka yi mutunci da girma a wajan wanda kaiwa afuwan Nan, haka duk Wanda yayi tawadu'u tabbas Yana tare da Daukaka._ Allah yasa mudace.
~*Akaramakallahu Bash-khan*~👳🏻♂️