YAR UWA INA ZA KI KAI WANNAN ZUNUBIN?

'YAR UWA INA ZA KI KAI WANNAN ZUNUBIN?





A lokacin da kike barci zunubi ake rubuta maki. 

Kina cin abinci ma zunubi ake rubuta maki. 

Kina sallah, hira, karatu, amma ana zunubi kike samu. Kin mutu ma kina cikin qabarinki ba ki tsira ba.

Kin san ta inda zunubin yake zuwa kuwa?

Hotuna (pictures) naki waďanda kika saka a social media tare da bayyana adonki ko wani sashi na jikinki, abin takaici ma sai ka ga mace musulma amma ta saka photo rabin Qirjinta a waje. To Wallahi ki sani! A duk lokacin da wani wanda ba muharraminki ba ya yi viewing din wannan photon sai an rubuta maki zunubi, shin za ki iya imagining na adadin mutanen da ke kallon wannan photon a kowace rana? Wani ma saving zai yi a wayarsa, kuma duk san da ya kalla sai kin samu zunubi. 

'Yar uwa idan kin kasance daga cikin irin waďannan matan masu saka pics ďinsu a social media wanda adonsu ko wani sashi na jikinsu ya bayyana, a yanzu kina da damar ki tuba zuwa ga Allah tare da neman gafararSa, kuma ki cire su. 'Yar uwa ina jin maki tsoron ki mutu amma kuma ba ki dinga samun zunubai ba, kina cikin Qabarinki, nan kuma duniya kin bar wani abin da kullum sai kin samu zunubi, me kike tunanin zai faru kenan? Ya haďuwarki da Allah za ta kasance tunda kin sa6a masa? Shin ba ki da sani dangane da Qarfafan mala'ikun nan waďanda ba su sa6a umarnin da aka ba su? Lallai ne ki ji tsoron Allah 'yar uwa! 

'Yar uwa! Meyasa za ki wawantar da kanki? Mace musulma tamkar Diamond ko Zinare take, a kullum so ake ta killace kanta saboda ita mai darajace kuma abar darajawa. Amma kin je WhatsApp ko Facebook kina wani posting photonki inda da sakarai da wawa duk za su gani, burinki bai wuce ki samu likes and comments ba, ana comments da kalamai na fitar kunya ke kuma kina qara jin dadi, to zuwa yanzu wani amfani kika samu daga waďannan likes da comments da kika samu? Bata lokaci kawai. 

Don haka ita mace mai daraja tsada gare ta, su kuwa gama-garin mata ga so nan sai ka gaji da gani a kyauta. Tir! 

Allah Ya sa mu fi karfin zukatanmu! 
.

*Ayyub Musa Giwa.*
*▫️ANSAR.*
06/03/2019.
*08166650256.*

*📚Irshadul Ummah WhatsApp.*
Post a Comment (0)