BACCI AKAN CIKI(Rub da Ciki) !!!



BACCI AKAN CIKI(Rub da Ciki) !!! 
.
Mutane da dama suna wannan kwanciya ta Rub da Ciki, Wanda mafi yawa suka mai dashi a matsayin kwanciyar da tafi musu dadi ba tare da sun san cewa kwanciya ce wacce ALLAH baya so Kuma Annabi (ï·º) yayi hani akan hakan ba, wasu daga ciki Kuma sun san cewa ba kyau Amma saboda son zuciya sai kaga suna yin irin wannan kwanciyar ba tare da sun damu ba.
.
Hakanan akwai wadanda daga anyi magana akan wannan kwanciya ta Rub da Ciki sai suce ai camfi ne (ma’ana maganganun mutane) ne kawai.
.
Toh a hakikannin gaskiya babu maganar chamfi, An samo Hadisi ingantacce daga hanin Manzon ALLAH (ï·º) akan ita wannan kwanciya ta Rub da Ciki kamar haka:
.
Annabi (ï·º) Yace: “Ita dai kwanciya (Rub da Ciki) kwanciya ce ta ‘Yan-wuta, Kuma kwanciya ce da ALLAH yake fushi da ita.” [Abu dawud ne ya ruwaito shi da Isnadi ingantacce]
.
Hakanan Hadisi ya inganta cikin sunani Abu dawud da Tirmizhi daga Ya'ish Bn É—uhfatul Gifari (RA) daga babansa cewa: wata rana Annabi ( ï·º ) yazo wucewa ya same ni a masallaci ina kwance rub da ciki sai ya zungureni da Æ™afarsa yace kada kana irin wannan kwanciyar saboda kwanciya ce da ALLAH yake fushi da ita.”
.
Hakanan masana bincike sun gano cewa Rub da Ciki wajen bacci Yana da matukar illa ga kashin gadon baya har ma idan an dade ana irin wannan kwanciya akan ciki Yana jawo babbar matsala har ta kai ga gocewa a kasusuwan bayan Dan-Adam, hakanan bincike ya nuna cewa nauyin mutum Yana tsakanin wuyar sa ne don haka kwanciya akan ciki na iya jawo jijiyoyi su matsu haka Kuma zai yi wahala gadon bayan mutum ya mike daidai idan ya kwanta ta haka wajen bacci. Wannan ke Kara tabbatar mana da cewa lallai dukkan abunda Musulunci yazo mana dashi na umurni ko hani toh lallai akwai fa’ida acikin sa.
.
Saboda haka idan mutum yasan Yana irin wannan kwanciya toh yayi kokari ya daina, Iyaye su ringa Sanya Ido a irin kwanciyar da yaransu suke yi su gyara musu Kuma su daura su akan turba na gaskiya.
.
ALLAH Yasa mu dace (Ameen)


Post a Comment (0)