FAƊAR AMEEN BAYAN GAMA KARANTA FATIHA ACIKIN SALLAH

FAƊAR AMEEN BAYAN GAMA KARANTA FATIHA ACIKIN SALLAH.


*An gafarta masa abinda ya gabata na zunubansa, ga wanda Fadar AMEEN din sa ta dace da ta MALA'IKA*

Daga Abi Hurairata رضي الله عنه, daga Manzon Allah صلى الله عليه وسلم yace;

_*(Idan Liman yace AMEEN to kuma ku fadi AMEEN, domin dukkan wanda fadar AMEEN dinsa ya dace da ta Mala'ika, to an gafarta masa abinda ya gabata na zunubansa)*._

Ibn Shihaab Allah yayi masa Rahama yana cewa;

*"Manzon Allah SAW ya kasance yana Cewa AMEEN"*.

@صحيح البخاري:{780}

Yana cikin KUSKURE ka fadi AMEEN da zarar kaji Liman yace ولا الضالين WALADH DHAALEEN, kai tsaye cewar Ameen kuskurene har sai kaji Liman ya fara fadar AMEEN Sai kaima ka fadi amin, ba wai ka bari ba har sai ya gama kace ameen ba, ba kuma ka riga shi fada ba, abinda yake daidai shine;

*"Da zarar ya fara fadar AMEEN kaima sai ka fada tare da shi dan ku dace da fadar AMEEN na Mala'ika"*.

ابْنُ بـَطّـالٍ -رَحِمَهُ اللّٰهُ تَعَالَىٰ-:
Yana cewa;

*"Dukkan wanda yake mai yawan zunubai da sabon Allah, kuma yake son Allah ya kankare masa wadannan zunubai ba tare da shan wahalaba, to ya lazumci zama awajan da ya gama sallarsa ta farilla bayan sallah, dan samun adduar Mala'iku mai yawa agaresa, da kuma nema masa gafara, kuma wannan lokacine da ake fatan amsa adduar bawa"*.

Allah yana cewa;

_*{وَلَا يـَشْفـَعُـونَ إِلَّا لِـمَنِ ارْتـَضَىٰ}*_

[الأنبياء/ ٢٨].

Kuma Manzon Allah SAW ya bamu labarin wanda fadar AMEEN dinsa ya dace da fadar AMEEN na Mala'ika, an gafarta masa abinda ya wuce na zunubansa.

Fadar AMEEN na Mala'ika suna fadane sau daya kuma yana dacewa da fadar AMEEN na Liman kuma adduar Mala'iku da neman gafararsu ga bawa yana ga wanda ya zauna yake ambaton Allah bayan sallar farilla, kuma wannan lokacin da ake kwadayin amsa adduar Allah ga bawa.

@شـرح صـحيح البــخاري، لابن بطـال؛ ج: (٣). ص: (١١٤).

*ALLAH NE MAFI SANI*

ALLAH BAMU IKON GYARAWA.

SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/DailyHadithss
Post a Comment (0)