HUKUNCIN MATAR DA TA GAYYATO JININ HAILA KAFIN LOKACINSA.

HUKUNCIN MATAR DA TA GAYYATO JININ HAILA KAFIN LOKACINSA.



*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikum, mallam ina hukunchin macen da in mijinta ya fitine ta da jima'i take shan magani don jini yazo mata, Yaya hukuncin jinin yaya kuma maganar sallah,? tunda gayyato jinin ta yi.  
:
*AMSA*👇
:
Wa'alaykumussalam To 'yar'uwa Allah da manzonsa sun rataya hukunce-hukuncen jinin haila ne da samuwarsa, kamar yadda aya ta: 222 a suratul-Bakara take nuni zuwa hakan, duk da cewa gayyato shi ta yi  saidai zai dauki dukkan Hukunce-hukuncen haila, mutukar ya zo da saffar sa.

Gayyato jini saboda hana miji jin daɗi bai dace ba, saboda duk dabarar da za ta kai zuwa haramun to ita ma ta zama saɓon Allah, Ya wajaba ga mace ta baiwa miji kanta duk lokacin da yake bukata, in ba tana da uzurin da sharia ta yarda da shi ba, don haka bai kamata mace ta hana mijinta saduwa da ita ba ta hanyar yin dabara.
             
Allah ne mafi sani.

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)