IYAYE NA SUN HANANI AURE WAI SAI NAYI MAKARANTA

IYAYE NA SUN HANANI AURE WAI SAI NAYI MAKARANTA



*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikum. Malam ga wata tambaya ta sister na, amma fa tana da nauyi malam se ka daure zaka iya bamu ansa. Iyayen mu sunki suyi mata aure sunce dole se taci gaba da karatu, toh shine take ceman wai ta hanyar tunani take biyan sha'awar ta, wani lokacin kuma in suna waya ne da wanda take so din kuma ba wai suna maganar kauce hanya bane, kamar dai yanda tace man. Tace man bata iya tambaya a islamiyar su don kar agane itace, shiyasa na tambayeka, gashi sun anshe wayar ta. Babban abun tambayar ta shine Wai hakan ma istimna'i ne kenan?
:
*AMSA*👇
:
Wa,alaikuussalam to shima yana shiga cikin istimina'i, saboda shima biyan buqata ne ta hanyan da be dace ba.
Dukka sun shiga cikin ayoyi uku, da suke cikin suratul Ma'arij.
ﻭَﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻫُﻢْ ﻟِﻔُﺮُﻭﺟِﻬِﻢْ ﺣَﺎﻓِﻈُﻮﻥَ) 29 )
Wadan da suke, ga farjojinsu, masu tsarewa ne.
ﺇِﻟَّﺎ ﻋَﻠَﻰٰ ﺃَﺯْﻭَﺍﺟِﻬِﻢْ ﺃَﻭْ ﻣَﺎ ﻣَﻠَﻜَﺖْ ﺃَﻳْﻤَﺎﻧُﻬُﻢْ ﻓَﺈِﻧَّﻬُﻢْ ﻏَﻴْﺮُ ﻣَﻠُﻮﻣِﻴﻦَ ‏( 30 )
Saifa akan matan Auren su da abinda hannayen su na dama suka mallaka. To lalle ne sukam ba wadanda ake zargibane.
ﻓَﻤَﻦِ ﺍﺑْﺘَﻐَﻰٰ ﻭَﺭَﺍﺀَ ﺫَٰﻟِﻚَ ﻓَﺄُﻭﻟَٰﺌِﻚَ ﻫُﻢُ ﺍﻟْﻌَﺎﺩُﻭﻥَ ‏( 31 )
To duk wanda yanemi abinda yake a bayan wannan, to wadanchan sune masu Qetare iyaka.
wadan nan ayoyin suna nuni akan dukkan wata hanya da mutum ze bi, ya biya buqatan shi na hanyan halak da haram.
Idan mutum ya biya buqatan shi ta, hanyar hannu, ko kallo,ko magana ko wani hanya daban.
Matuqar dai an tsallake wannan iyaka da ALLAH yafada, to anshiga Matsala.
Kunga yanxu kuma hanya ɗayan ta rage shine, hanyan yin Aure!!.
:
To yanxu kuma dayawa daga cikin iyaye suna buqatan toshe Wannan hanyan (wato hanyar Aure).
Rashin wayewa ne ace baza'a Aurar da mace ba, wai seta gama makaranta.
To idan ta gama makaranta da zaran ta samu aiki, sai samari su gudu!!! kafin ku laburta harta kai shekara 30 a gida.
To yaya zakuyi da ita, wannan za ta daure kenan batayi zina ba.

Ranan 15-09-2016 aka kama wata da wani, su dauki kimanin shekara 2 suna zina, saka makon An hana su Aure! Daga Qarshe mahaifinta ya kamo da ciwon zuciya me tsanani!!!
Wata Qissa da take ban tsoro!! labarin ya faru ne a Qasar saudiya, macece mahaifinta ya hanata Aure! har lokacinda ta gama makaranta duk lokacinda aka zo neman Auran ta, se yakie saboda yanason albashin da take dauka!!!
A Kwana atashi se da ta kai kusan 35 in bata fi ba, kuma mace ce me kyau me ilmi addini, tayi hakuri ta jure bata ta6ayin zina ba.
Bayan Qawayen ta kusan duk sunyi Aure har wasu sun kusa Aurar da yaran su.
Itakuma damuwa da abubuwa suka mata yawa har takaiga rashin lafiya, aka bata gado a asibiti, setasa aka kira malaman ta suka zo ga mahaifinta a gefenta, setace Baba zanyi Addu,a kace Amiiin, bayan ta gama addu,a a zuciyan ta tace kace amiiiin yace amiiin.
Tace baba kasan me na Roqa yace a'a tace na roki ALLAH ya hanaka jin daɗin rayuwan lahira sama da yadda ka hanani jin dadin rayuwan duniya!!!
Daga wannan bata sake wani jawabi ba!!! ta mutu,
nikam ko kadan banaga laifin ta wallahi kuma duk wanda ya dau wannan salon wallahi bazan hana shi ba.
Inzaku Aurar dasu ku Aurar inkun qi maganan Manzon ALLAH ya tabbata shine "zaku haifar da fitina a doron Qasa" sune zinace zinace da kisan kai, dan a duk lokacinda akayi zina, da kyar in kisan kai bai biyo baya ba, saboda tin ɗan yana ciki za'a kashe shi.
Wani Kuma daga zaran yaga karuwan shi da wani, se ya dau matakin kashe wanchan.
Wallahi fitin tunun dasuke Qarqashin hana 'ya'yan ku Aure, ba qaramin fitina bane.

Dan haka ko ku gyara ko a shiga matsala.
Ko ayar Kur'ani da nassin hadisi basu zama muku aya ba, ai yakamata karan kanku kusan akwai wa'zi a ciki.
Duk wanda yake hana yayan shi Aure seya samu wasu Qa'ida irin wannan,Wallahi shi bazai iya hakura da matan shi na wata ɗaya ba, ko wani abu makaman cin haka, Amma dan son duniya kawai se su hana mutane Aure, suta cutar da al-ummah.

Lalacewan me Addini yafi tashin booom!

ALLAH YA TSARE MU.

TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)