KE CE SARAUNIYA

KE CE SARAUNIYA 
--------------------------------


Imam Qurtubi (r) yana cewa:

 Matsayin mace musulma mumina a cikin Aljanna ya fi na Hoorul-A'yn. (Mace mumina) Tana da matsayi mafi girma kuma mafi kyau.
 
Mace saliha da ta kasance daga mutanen Duniya, idan ta shiga Aljanna ta shigeta ne a sakamakon ladan aikin alherinta da kuma daukaka daga Allah akan addininta da kyautatawar ta (acikin duniya).

 Amma ita matar Hurul ayn ta kasance ne daga nau'in jin dadin Aljanna, an halicce ta ne acikin Aljanna domin wasu, kuma an sanya ta ne a matsayin lada ga mumini akan ayyukan alherinsa.
 
Akwai bambamci mai girma tsakanin wacce ta shiga Aljanna a matsayin sakamakon aikinta na alheri da wanda aka halicce ta a matsayin sakamako ga wanda yayi aikin kwarai.

 Ta farko salihar mace ce, wacce take sarauniya mai girman matsayi. Ta biyun kuma ita ce Hurul A’yn duk da cewa tana da matsayi mai girma da kyan gani amma gwargwadon fahimtar mutane, matsayinta yana qasa da na sarauniyar. kuma ita tana bin umarnin ubangidanta ne wato namiji mumini, domin Allaah ya halicce ta ne a matsayin sakayya na lada a gareshi.
 [Tafsirin Qurtubi, (16/154)]

#Zaurenfisabilillah

Telegram:
https://t.me/Fisabilillaaah

Instagram:
https://www.instagram.com/zaurenfisabilillah/
_____________
Post a Comment (0)