SU SUKA FI CHANCHANTAR KYAUTATAWAR KU

SU SUKA FI CHANCHANTAR KYAUTATAWAR KU



Ash-Shawkaani (r) ya ce:

Hakika daga cikin mutanen da suke da matsayi mafi girma wajen kyautatawa kuma suka fi cancanta a siffanta su da gaskiya sune wadanda suka fi kowa alheri ga iyalansu. Lallai iyalai da dangi sune wadanda suka fi kowa hakkin farin ciki da jin dadi, da (mu'amala cikin) kyawawan dabi'u da kyautatawa. Tare da fa'idantar dasu da tunkude cutarwa daga gare su. Idan mutum ya kasance haka, to, shine mafi alkhairin mutane. Idan kuma ya kasance kishiyar hakan to yana kan wani bangare na sharri.

Akwai da yawa daga cikin mutanen da suka fada cikin wannan mawuyacin hali, don haka sai ka ga mutum idan yana tare da iyalansa shi ne mafi sharrin mutane a cikin halaye, mafi wahala kuma mafi muni a wajan kyautatawa. Amma idan ya hadu da wadanda ba iyalansa ba, sai ya zama mai taushin hali da jin kunya, yana da kyawawan dabi’u, kuma yana inganta kansa, kuma alherinsa yana karuwa. Ko shakka babu wanda ya kasance haka to an qangeshi daga samun nasara kuma ya kauce daga hanya madaidaiciya. Muna rokon Allaah ya shiryar dashi
   [Naylul Awtaar : 8/121]

#Zaurenfisabilillah

Telegram:
https://t.me/Fisabilillaaah

Instagram:
https://www.instagram.com/zaurenfisabilillah/
Post a Comment (0)