MAFITA (01

MAFITA (01)


بسم الله الحمد لله والصلاة والسلام على رسول الله وعلى آله وصحبه أجمعين والتابعين لهم بإحسان إلى يوم الدين.

Rubutun *MAFITA* wani irin rubutu ne mai dauke da takaitaccen bayani game da Jinnul Aashiq da kuma hanyar da ake bi domin samun waraka da Izinin Allah cikin tsarin da Addini ya yarda da shi.

Jinnul Aashiq wani nau'i ne na Shaidanin Aljani da yake da wuyar sha'ani kuma yakan iya shafar kowane irin jinsin mace ko namiji, yawanci jinsin aure yake shafa kamar: Macen Aljani ta shafi Namijin mutum, ko Namijin Aljani ya shafi Macen mutun, amma kuma ana iya samun akasin haka a wasu lokutan.

Babbar alamar da take nuna ko take sanya a fahimci shafar Jinnul Aashiq ga karamar yarinya itace kamar haka:

Za aga yarinya ta kwanta da tufafinta da daddare amma sai aga ta wayi gari babu tufafin nan a jikinta, abin mamakin ma sau da dama yarinyar da ba ta iya cire tufafinta da kanta a zahirance ne abin yake faruwa da ita haka.

A irin yanayin ne idan har iyaye basu ankara sun dau matakin gyara ba yadda Shari'a tayi tanadi ba sai kaga yarinya ta girma tare da Aljanin ajikinta kuma tayadda raba su ba ƙaramin aiki bane sai da yarfe gumin goshi saboda ya saba da ita. Taimakon farko da yakamata arika yiwa yara domin kange su daga kamuwa da irin wannan mummunan bala'in na shaidanun Aljanu ko kambun baka shi ne: 

Koyawa yara su iya Karanta Ayatul Kursiyyu, kuma a nuna musu su rika karanta ta a ko da yaushe Musamman ma idan za su kwanta bacci.

A rika sanyawa yara tufafin da zai rika rufe musu tsiraicinsu, a daina ganin ai yara ne me ma za'a iya gani a jikin na su har ayi sha'awarsu... a'a ba haka lamarin yake ba Saboda gudun shafar irin shedanun nan ko kuma yin tasirin kambun baka ne yasa Addini yakoya mana yadda za muyi domin gujewa irin haka .

A rika karanta musu wannan Addu'ar : 

أعوذ بكلمات الله التامة من كل شيطان وهامة ومن كل عين لامة

"A'uzu Bi kalimatillahi Attaammah min kulli shaidanin wa haammah wamin kulli ainin laa maah."

Wannan Addu'a itace wacce Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yakasance yana nemarwa jikokinsa Hassan da Hussaini tsari da ita, Kuma yace: ita ce Babanku Annabi Ibrahim ( Alaihissalam) yake nemarwa Annabi Isma'il da Annabi Ishaaq tsari da ita."

Lallaikam idan mutum ya rike Abubuwan da Shari'a ta koyar wajan nemarwa iyalansa kariya ba shakka shi ne tsararre saboda ya nemi tsari ne da tsarin ALLAH ba wanin Allah ba.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani. 

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu'ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu.😍)

Domin karin bayani:
👇👇👇

Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu'aym)

Gmail:
rismawy86@gmail.com

WhatsApp :
+2348031542026

Telegram Channel:
https://t.me/Rismawymedicine
Post a Comment (0)