TSOKACI

TSOKACI




Dan uwa! 
'Yar uwa! 

Idan ka shiryu babu wanda shiriyarka za ta amfanar fiye da kai, Likewise idan ka lalace babu wanda lalacewarka za ta cutar fiye da kai! Wannan ya ishe ka abin tunani yayin da ka ga malamai suna ta kai komo don ganin ka bi Allah da ManzonSa, a dai-dai lokacin da kai kuma duniya da ma'abotanta suke ruďarka da abin da zai zamo maka abin tuhuma a ranar da aikinka kaďai zai ku6utar da kai. 

Gaggauta rabuwa da duk mutumin da ka kasa fahimtar amfaninsa gare ka, rungumi waďanda suke kokarin kusanto ka da Mahaliccinka, sai ka wayi gari a cikin mutanen kirki abin kwatance ☺ 

Barka da safiya. 

*✍🏿Ayyub Musa Giwa.*
*▫️ANSAR.*
*14th April, 2019.*

*📚Irshadul Ummah WhatsApp.*
Post a Comment (0)