MAFITA {02}

MAFITA {02}


Bayan iyaye da masu kula sun tsaya wajan tarbiyyantar da yaransu karanta Addu'o'in neman tsari waɗanda Shari'a ta inganta su kuma ta tabbatar da su, sai kuma su yunkura wajan nuna musu abubuwan da shari'a ba ta so kuma ba ta maraba da su, hasali ma su ne ke jawo iskokai, makarai ko kuma Aljanu su aboci mutum ta ko wacce irin fuska kamar: 

- Sanya tufafin da basu dace da Shari'a ba.

- Kallace-kallacen abubuwan da Shari'a take kyama kuma ta haramta, da dai sauransu.

Munji wasu daga cikin alamomin da ake gane Jinnul Aashiq na tare da karamar yarinya, shin ya za ayi kuma a gane alamar Jinnul Aashiq ga budurwa wacce batayi Aure ba kuma me ke kawo su?

Farko dai ya kamata mu san irin dokokin da Shari'a ta gindaya mana, musan abinda ALLAH yake so da wanda ba ya so, sai mu aikata wanda yake so kuma mu guji wanda ba ya so, saboda babu abinda Shari'a ta bari batayi bayaninsa ba kuma Manzon Allah salllahu alaihi Wasallama bai bar duniya ba sai da ya nuna mana duk wani Alkhairi domin mu jibince shi kuma mu aikata shi, kuma ya nuna mana duk wani sharri domin mu guje shi kuma kar mu aikata shi.

Insha ALLAHu a rubutu nagaba za muji abubuwan da ke jawo Jinnul Ashiq su shafi budurwa wacce batayi aure ba.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani. 

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu'ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu.🤲🏻)

Domin karin bayani:
👇👇👇

Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu'aym)

Gmail:
rismawy86@gmail.com

WhatsApp :
+2348031542026

Telegram Channel:
https://t.me/Rismawymedicine
Post a Comment (0)