MAFITA {03}
Daga cikin abinda ke jawo shafar Jinnul Aashiq ga budurwa wacce batayi aure ba, ga kadan daga cikin alamomin nan:
1- Fitar da tsiraici, ta rika shiga ta banza, ko kuma ta sanya tufafi amma kamar bata sanya ba, saboda surorin jikinta sun bayyana, ( domin su jinsin maza Aljanu sunfi sha'awar jinsin mata na mutane sama da yadda jinsin maza na mutane ke sha'awar jinsin mata na mutane yan uwansu).
2- Barin kai abude indai ba da wata sananniyar lalura ba, sai kaga ko kanta ne abude ko wani bangare na gashin kanta ya fito waje, sai kaga su Aljanun sun fitinu da ganin gashinta ya basu sha'awa, sabanin jinsin mutane maza ba kasafai ganin gashin mace ke sanya su fitinu da ita har suyi sha'awarta ba. Shi yasa Addini ya hana mace ta rika bayyanar da gashinta ga wadanda ba muharramanta ba.
3- Rashin yin Addu'a idan za'a shiga Toilet (Ban daki).
4- Rashin yin Addu'ar tube/cire tufafi ( Akalla ki/kace *Bismillahi* idan za a cire riga ko hijabi ko wando ko makamantan su), domin ita "Bismillahi" ALLAH yana sanya katanga tsakanin idanuwan shedanu da kuma al'aurar mutum, ta yadda su Shedanun ba za su iya samun damar ganin al'aurar mutum ba balle har su samu damar cutar da duk wanda ya furta ta kafin ya cire tufafin sa ba.
5- Yin istimna'i ( Mutum mace ko namiji su rika biyawa kansu bukata da hannu ko da wani abu makamancin haka, har a gamsu ko akasin haka).
6- Zancen batsa ta ko wace irin sifa da kuma kallon batsa.
7- Kauracewa karatun Alqur'ani da Azkaar na safiya da maraice da kuma wajan kwanciya bacci da kauracewa saurarar wa'azi da Kuma yawan sauraron kade-kade da wake-wake.
8- Bayyana kwalliya ga jama'a a makaranta ko a waje ko kuma a kasuwa ko dora hoto a social media tare da bayyanar da wani bangare na kwalliyar ki a fuska ko a hannu ko makamantan haka, ( Kamar mace tayi lalle a hannunta ko a kafarta har ta rika bayyanar da su ga jama'a ko a social media) , a Irin haka ba wai iya mutane ne kaɗai za su kalla ba har Aljanu ma suna kalla kuma idan kin ba su sha'awa sai su shafe ki su cutar da ke. Allah ya kiyaye.
9- Rashin kamun kai ga mace yazamto kowa kulawa take, tayi ta cin chewing gum akan hanya ko tana tafiya tana ciye ciye ko tarika shekewa da dariya abinta, yin hakan yana iya sabbaba mata shafar shedanu.
10- Wata kuma za kaga tana kiyaye duk wannan abubuwan daidai gwargwado amma kuma sai ka same ta da Jinnul Aashiq, to ita wannan ana sa ran Sihiri ne aka yi mata ko kuma Qaddarar tace Allah ya rubuta ba makawa sai hakan ta same ta a rayuwa, duk cikin jarabawa ne. ALLAHu A'alam.
Wannan kadan kenan daga cikin abinda ke janyowa mace Jinnul Aashiq ko sihiri har suyi tasiri ajikinta, yanzu wace Alama ce mace za ta iya ganewa tana da shafar Jinnul Aashiq ajikinta?
Insha ALLAHu za muyi bayanin haka a gaba.
Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.
Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.
(Ayi mana Addu'ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)
Domin karin bayani:
👇👇👇
Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu'aym)
WhatsApp
+2348031542026
Gmail:
rismawy86@gmail.com
Telegram Channel:
https://t.me/Rismawymedicine