AN YIWA MAHAIFIYARSA SHARRIN MAITA



AN YIWA MAHAIFIYARSA SHARRIN MAITA
:
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikum malam inai maka fatan alkairi dan allah malam Nine aka yiwa mahaifiyata sharrin maita har mukaje kotu bayan munje kotu sai mutanen suka bamu hakuri.

To har yanzu idan na tuna wannan bakin ciki yana hanani nutsuwa. Dan Allah Malam atemaka min da wata addu'a da zan dinga yi.

Kuma malan menene makomar mutumin da aka yiwa sharri yayi hakuri a addinin islama? nagode 
:
*AMSA*👇
:
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. 

Hakika dukkan muminai suna da alfarma mai girma agun Allah. Kuma saboda wannan ne Allah ya haramta yin mummunan zato ko zargi ga bayinsa muminai. Allah yace. :

"YAKU WADANDA SUKA BADA GASKIYA!! KU NISANCI MAFI YAWAN ZATO, DOMIN HAKIKA SASHEN ZATO ZUNUBI NE. KADA KU RIKA BINCIKEN LAIFUKAN JUNANKU, KADA SASHENKU SU RIKA GULMAR SASHE.."

Acikin wannan ayah mai girma Allah ya hana mummunan zato, da kuma binciken laifukan mutane, da yin gulmarsu. 

Abdullahi bn Umar (rta) yace naga Manzon Allah ﷺ yana yin dawafi adakin Ka'abah sai najishi yana cewa : "Mamakin tsarkinki da tsarkin Qamshinki! Ina mamakin girmanki da girman alfarmarki, amma ina rantsuwa da wanda numfashin Annabi Muhammadu ﷺ ke karkashin ikonsa, wallahi mutuncin mumini yafiki girma da alfarma awajen Allah, da dukiyarsa da jininsa, kuma kada ayi masa wani zato (shi muminin) sai na alkhairi".

(Ibnu Maajah ne ya riwaitoshi akan lambar hadisi na 3932).

Don haka tunda suka keta alfarmar mahaifiyarka, suka ci mutuncinta suka munana zargi gareta, hakika sun zalunceta kuma duk wanda aka zalunceshi yayi hakuri, ladansa yana wajen Allah. Idan kuma yayi addu'a to Allah zai amsa masa kuma zai taimakeshi akan wadanda suka zalunceshi. 

Duk lokacin da kaji wannan bakin cikin ya lullube zuciyarka, kayi alwala kayi sallah ka roki Allah ya baku mafita kuma ya yaye muku wannan damuwar. Sannan ka yawaita wannan addu'ar :

اللَّهُمَّ رَحْمَتَكَ أَرْجُوفَلَا تَكِلْنِي إِلىَ نَفْسِي طَرْفَةَ عَيْنٍ، وَأَصْلِحْ لِي شَأْنِي كُلَّهُ، لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ

Allaahumma rahmataka 'arjoo falaa takilnee 'ilaa nafsee tarfata 'aynin, wa 'aslih lee sha'nee kullahu, laa'ilaaha 'illaa 'Anta.

Da kuma wannan :

لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْت سُبْحَانَكَ إِنِّي كُنْتُ مِنَ الظَّالِمِينَ

LA ILAHA ILLA ANTA SUBHANAKA INNEE KUNTU MINAZ ZWALIMEEN.

Kayi hakuri, kuma kaci gaba da kwantar da hankalin mahaifiyarka ta hanyar kyautata mata, da sanya mata farin ciki. Allah yana tare da masu hakuri, kuma yana tare da masu tsoron Allah da masu kyautatawa. 

WALLAHU A'ALAM. 

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)