MU RIƘA SANIN NI'IMAR DA ALLAH YAYI MANA.

MU RIƘA SANIN NI'IMAR DA ALLAH YAYI MANA.



Daga Abi Hurairata رضي الله عنه yace, Manzon Allah ﷺ yace:

_*(Ku riƙa duba waɗanda suke ƙasa da ku, ku daina kallon waɗanda suke sama da ku wajan ni'ima, yin hakan zai sanya ku sannan Allah yayi maku ni'ima sannan kuma ku sami damar godiya ga ni'imar Allah)*_

@متفقٌ عَلَيْهِ، وهذا لفظ مسلمٍ

*ابن باز رحمه الله:*
Yana cewa:

*Mutum idan yana kallon wanda yafi shi yawan dukiya da abin duniya da kyau da matsayi da wanin wannan na daga cikin ni'imomin duniya, hakan zai kara masa guri da rashin kallon ni'imomin da Allah yayi masa ballantana ya godewa ni'imar Allah, sai dai kayi dubi ga na kasa da kai wanda ya fika talauci da rashin wadata da wanda bai kaika ba duniya da abin duniya ba, sai hakan ya sanya ka gane Allah yayi maka ni'ima har ka sami damar godiya ga ni'imar Allah, amma Wannan kan lamarin duniya ake nufi, banda lamarin lahira, amma lamarin lahira kana kallon wanda ya fika kokarin cikin ibada da kiyaye dokokin Allah, sai haka ya sanya ka kara dagewa cikin ibada..............)*

@شرح رياض الصالحين حديث (٤٦٧)

*Allah ne mafi sani.*

SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/DailyHadithss
Post a Comment (0)