MATSAYIN ZUMUNCI A TSAKANIN MUSULMI
Da sunan Allah mai yawan rahama mai Jin kai, Tsira da Aminci su kara tabbata da fiyayyen haliyya Annabin Rahama Sallallahu Alaihi wa sallam, da Alayensa da sahabbansa baki daya.
MA'ANAR SADA ZUMUNCI:
Sada zumunci shi ne kyautatawa da jinkai da bibiyar yan uwa (ma'abota zumunci), ta hanyar sadar da dukkan alheri gare su, da kawar da dukkan sharri daga garesu gwargwadon iko.
Ziyartarsu da amsa kira da gayyatarsu da taimaka musu da dukiya da tausasa magana gare su da kawar da kai daga kura-kuransu da yi musu addu'ar alheri, duk bangare ne na sada zumunci.
Har ila yau, yana daga ma'anar zumunci yin sallama ga yan'uwa yayin haduwa da gaishesu, haka zalika yana daga cikin Sada Zumunci gaisheda mai Atishawa da ce masa Yarhamukallahu”.
Sannan zuwa duba dan'uwa mara lafiya da jajanta masa kan wata asara da ya yi da taya shi farin cikin samun wani alheri da rufa masa asiri da rike amanarsa da kare mutunci da martabarsa a kan idonsa ko a bayan idonsa a boye ko a bayyane da yi masa nasiha da bashi shawara ta alheri duk suna cikin sada zumunci.
FALALAR SADA ZUMUNCI DA UKUBAR MAI YANKESHI.
Sada zumunci yana da tarin falala, wanda idan muka dauke falalar da za a samu a lahira, zamu ga cewa tun daga duniya idan kaje ka sada zumunci koda ziyarar abokin ka ne ko wani dan'uwanka na jini, zakaji ka samu nutsuwa da nishadi, shima kuma zai ji dadi sosai.
Kamar yadda aka sani duk abin da akayi umarni da shi a cikin ayyukan addini ana samun falalarsa idan aka aikata, sannan kuma ana samun ukuba idan aka ki aikatawa.
FALALAR SADA ZUMUNCI
1. Hadisin Nana Aisha Allah ya kara mata yarda tace, Sada zumunci yana rataye ne da Al-Arshi, yana cewa: wanda ya sadar dani to zan sadar dashi, wanda ya yanke ni to zan yanke shi (Bukari da Muslim).
Ma'ana shine zai sadar dashi da Rahmar Allah (SWT) ko ya yanke shi daga samun Rahama.
2. Manzon Allah (SAW) yace: Ba Sadar da zumunci bane in anzo maka kaje, in an baka ka bayar, in an girmamaka ka girmama, Sada Zumunci shine wanda ya yanke maka ka Sadar masa ( wato Ka ziyarci wanda baya ziyartarka, ka bawa wanda ya hanaka.)
UKUBAR MAI YANKE ZUMUNCI
1. Hadisin Zubair dan Mad'im Allah ya kara yarda a gareshi yace, Hakika Manzon Allah(SAW) yace: Mai yanke zumunci bazai shiga aljanna ba. (Bukari da Muslim).
2. Hadisin Abi Bakrata Allah ya kara yadda a gareshi yace Manzon Allah(SAW) yace: Babu wani zunubi wanda ya cancanta Allah ya gaggauta yiwa mai shi ukuba tun daga nan duniya bayan wanda ya tanada a lahira kamar mai yanke zumunci (Bukari).
Duk wanda ya yanke Zumunci ga makusantansa raunana (wato Talakawa mabukata) ya kaurace musu, baya sada Zumunci a garesu, baya kyautata musu, alhali yana da iko da wadatar da zai taimaka musu, to wannan haramun ne shiga Aljanna a gareshi, saidai in ya tuba ga Allah, ya dawo ya kyautata musu.
Mai yanke Zumunci tun daga duniya yan'uwansa baza su sami shakuwa da shi ba, kuma har ma wani lokacin a rika mantawa gaba daya. Ya Allah ka bamu ikon sada zumunci domin saduwa da dukkanin alkhairan da ke cikinsa na duniya da lahira.
Malamai sun bayyana Sada zumunci a matsayin daya daga cikin manyan Alhairan da ake gaggauta bayar da lada akai, kamar yadda yazo a cikin Hadisin Manzon Rahama Annabi Muhammad (SAW) ya ce: Alherin da ake gaggauta bayar da lada a kai shi ne Sadar da zumunci.
Abin da Manzon Allah (SAW) yake kokarin nuna mana shi ne Musulmi ya kasance a koda yaushe mai tsananin kula da yan'uwansa na jini, dangi gami da yan'uwa na ruhi, wato wadanda addini ya hada su.
Sannan Addinin Islama ya kara fadada zumunci ta hanyar sababi, wato aure, domin a cikin da'irar aure, addinin Musulunci ya tsara ingantacciyar hanyar sada zumunci, ta yadda ma'aurata ke kara fadada yan'uwantaka daga nesa zuwa kusa. A lokacin da ka auri mace, iyayeta da yan'uwanta da dukkan danginta sun zama yan'uwanka na jini. Haka kai ma dukkanin danginka sun zama nata tare da hakkin sada zumunci a tsakaninku.