MUSULMI SUNA BUƘATAR WAƘA
Ita Waqa a Musulunci ba Haramun bace, Waqa matsayinta matsayin Magana ce, kamar yadda ya tabbata acikin Hadisin Bukhaariy, Annabi SAW yake cewa: ((Daga cikin Waqa akwai wadda take akwai Hikima acikinta, akwai Ilimi)).
Innama Waqa da za'a haɗata da Kiɗa ko Tafi ko makamantan haka ita ce ɓarna, kamar yadda Allah Yace: ((Ba kowa ke binsu ba sai ɓatacce)).
Su Waqoqi nau'i biyu ne:
i) Akwai ta Halal
ii) Akwai ta Haram
Dukkan Waqoqin da suke ɗauke da cin-mutunci ko Batsa ko wasu abubuwa waɗanda basu dace da Addinin Musulunci ba, waɗannan Waqoqi Malamai sun tabbatar da cewa Haramun ne. Waqe ya halatta shima kar a haɗa shi da Kiɗa!!!
Amma abun nufi da Musulmi suna buƙatar Waƙa anan shine: akan samu Ƴan Bidi’ah Ɓatattu, kamar Ƴan Shi'ah suka ƙirƙiro Waqoqi domin su ƙarfafi wasu abubuwan na Tarihi, kamar waɗanda suka ƙirƙira suka jingina ma Sayyiduna Aliyu (RA) ko su jingina ga Nana A'isha da sauran Sahabbai, don haka a madadin yi musu Raddi a rubuce sai mu ma cikin Musulmi a samu wani ya mayar musu da martanin shirɓaguwar su a Waqe don ya zama an mayar da martanin da irin abunda suka kawo don su rikita Tarihin. Don haka, Waƙa tana daga cikin Makamai da ake Yaƙar ɓatattu da ita don a tabbatar da Sunnah
Babbar Qa'ida dangane da Waqa itace: Me ke cikin Waƙar? Abunda ke cikinta shi ke hukunta ta.
✍ *ANNASIHA TV*
```(Don't Forget to like, follow, Subscribe and Share, Jazakumullahu Khairan)```
*Facebook Page*
https://www.facebook.com/annasihatv/
*Telegram Channel*
https://t.me/AnnasihaTvChannel
*Instagram Account*
https://instagram.com/annasihatv?igshid=1pq1vxrx3ubp6
*Youtube Channel*
https://www.youtube.com/AnnasihaTvChannel
*Twitter Handle*
https://twitter.com/AnnasihaTv?s=09
*TikTok;*
https://vm.tiktok.com/ZMeYYVnPP/
*Call:*
+2348063836963 +2348142286718
*Email:*
islamisannasiha@gmail.com