MATA 'YAN WAHALA

{MATA 'YAN WAHALA}🤔🤔.


Kullun baku da aiki, sai neman maganin kara kiba, maganin kara hips, maganin kara nono,maganin rage tumbi, duk ku hana kanku sukuni, a dayan bangaren kuma wata maganin rama take nema, maganin rage nono, da a sauransu.

Meke kawo haka? Mijin da zan aura have yana son mace mai nono, mai hips, na cika siranta da dai sauransu, ko kuma kin cika kiba ki rage, wata kuma ma mijintane zai ce haka, duk akan mene, bai gode ma Allah akan halittarki ba,.

Duk yanda kika ga halittarki haka Allah yake son ganinta, bawai maza suyi ta samu wahalar banza ba don kawai biyan bukatarsu da jin dadinsu, in abun banza ne su suyi mana, kin taba ganin namiji na neman maganin fadin kirji, ko kuma na saje,a'ah sai mu 'yan wahala.

Ga shawara , a duk sanda kika hadu da miji ko saurayi mai wannan halin, kema ki samu wani abu na jikinsa kice masa ya kara ko ya rage, fakat idan abun saukine dashi.

A rayuwarnan kaso mutum don addininsa da halinsa, bawai don surarsa ba, saboda day by day, sai abun nan da kake so ya samu nakasu.

Masu mazaje wadanda suke complain nono ya zube, dena tada hankalinki, nuna masa ai shi ya zubar dasu ba wani ba, da zasu damu mutane haka, in ya dameshi, kema ki ce masa ya rage tumbi, ko kuma ki ce AK47 dinsa bata kawo miki yanda kikeso shima ya nemi magani.

Matar Abdoul✍️

Pls kuyi sharing wadansu group din.
Post a Comment (0)