SHIN YA HALASTA MUTUM YACI TAFARNUWA YAZO MASALLACI

SHIN YA HALASTA MUTUM YACI TAFARNUWA YAZO MASALLACI ?
:


*TAMBAYA*❓
:
Asslamu alaikum warahmatilla malam ina yimaka fatan Alkhari, shin malam akwai hadith dayazo daga manzon Allah (saw) duk wanda yaci tafarnuwa karyazo masallaci harsai ya wanke bakinsa Malam ina neman karin bayani dakuma wanda ya rawaito Ngd.
:
*AMSA*👇
:
Wa'alaykumussalam, 

Akwai hadisin Abdullahi dan umar wanda ke cikin swahihul Bukhari 853. Manzon Allah saw yace:- 
*_“Duk wanda yaci wannan itaciyar (yana nufin tafarnuwa) toh kada ya kusanci masallacin mu”_*

A wani lafazin wanda imam muslim ya fitadda shi 561,.. 

*_"kada yaje masallatan mu”_* 

Yazo cikin Swahihul Bukhari 855 har'ila yau da muslim 564 manzon Allah yace :-

*_"Duk wanda yaci tafarnuwa ko albasa toh ya kaurace mana”_* a wani wurin *_”Ya kauracewa masallacin mu, sai ya zauna a gidansa.”_*

Don haka wasu malamai sun dauki hadisan a matsayin karhanci wasu kuma sun dauke su a matsayin haramci.

*Wallahu A'alam.*

✍️ *Malam Nuruddeen Muhammad* (Mujaheed) 

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)