MIJINA YACEMIN NA AJIYE AZUMINA BAYAN NAƊAUKA

MIJINA YACEMIN NA AJIYE AZUMINA BAYAN NAƊAUKA.
:


*TAMBAYA*❓
:
Assalamualaikum yaya inada tambaya Mace ce tadau Azumi sai mijin ta ya kira ta yace mata yana zuwa kuma inyazo ba kwana zai yi ba sai yace ta Aje Azumin shin zata bishi ne ta Aje ko kawai takai Azumin ta?
:
*AMSA*👇
:
Wa alaikumussalam warahmatullah wabarakatuhu 

To hadisi ya tabbata daga Annabi Sallallahu alaihi Wasallam cewa "kada mace tayi azumi alhalin mijinta yana nan, awasu ranaku inba na ramadan ba, saida izininsa" Bukhari yarawaito ahadisi mai lamba 5195, Muslim kuma 1026.
.
Amma idan miji bayanan mace tana iya daukar azumin nafila, idan kuma tana tsoron zai iya dawowa kowane lokaci a irin wannan zamanin da akwai wayar salula, zata iya kiranshi domin kawarda kokwanto, amma koda bata kiraba zata iya yin azuminta, amma idan yadawo na buƙaceta to kawai ta karya azumin, domin amsa kiransa wajibine indai batareda wata lalura ba, shikuma azumin ba wajibi bane 
.
Allah yasa mudace

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)