ZAN IYA KARA GASHI, SABODA MIJINA?

ZAN IYA KARA GASHI, SABODA MIJINA?



:
*TAMBAYA*❓
:
Malam na yi rashin lafiya kaina ya kwakuye, mijina yana bakin ciki, in ya ga kaina, zan iya kara gashi, don zaman auranmu ya kara dadi ? 
:
*AMSA*👇
:
To 'yar'uwa wata mace ta je wajan Annabi s.a.w. ta ba shi labari cewa : 'Yarta ta yi rashin lafiya gashinta ya fadi, kuma gashi mijinta ya umarceta da ta kara mata gashi, shin za ta iya karawa ? sai Annabi s.aw. ya ce mata : A'a, saboda an la'anci masu kara gashi" Bukhari ne ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 4831 .

Hadisin da ya gabata, yana nuna cewa : bai halatta mace ta kara gashi ba, ko da kuwa mijinta ne ya umarceta, saboda hakan zai sa ta shiga tsinuwar Allah .

Allah Ne Mafi Sani

Jamilu Zarewa

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)