ZUHUDU (GUDUN DUNIYA)

ZUHUDU (GUDUN DUNIYA)


Daga wa'azozi da hikimomin Shugaban muminai Imam Ali bn Abi Talib (a.s):

"الزّاهد في الدّنيا من لم يغلب الحرام صبره ولم يشغل الحلال شكره"

"Mai gudun duniya shi ne wanda haramun bai yi galaba a kan hakurinsa ba, kuma halal bai shagalar da shi daga godiyarsa ba".
(Tuhaful-Ukul shafi na 200).

Hakikanin gudun duniya a mahangar (addinin) Musulunci, wanda kuma Jagororin shiriya tsarkakan Imaman Ahlulbaiti, amincin Allah ya tabbata a gare su, suka yi wasici da shi kamar yadda wannan ruwaya ta nuna abubuwa biyu ne: 

1-Na farko shi ne mutum ya yi kokarin ganin waswasin Shaidan da karkata zuwa ga dabi'ar dabbobi da suke sanya mutum aikata laifuka ba su yi galaba a kansa ba, sannan kuma yayi tsayin daka da hakurin kaurace musu.

2-Na biyu shi ne: Kada ya bari ni'imar Ubangiji ta dauke masa hankali har ta shagaltar da shi daga barin godiyar Allah. Wato kada mutum ya zama maras godiyar Allah da kuma mancewa da wanda ya arzurta shi da wadannan ni'imomi. 

Abin lura a nan shi ne wannan sha'afa ta mutum babu yadda za ta ja shi in ban da zuwa ga kwari mai hatsarin gaske.

SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/DailyHadithss
Post a Comment (0)