NASIHAR WATA UWA MAI HANKALI GA 'YARTA YAYIN AURENTA

NASIHAR WATA UWA MAI HANKALI GA 'YARTA YAYIN AURENTA


1 - Ki zama kamar baiwa ga mijinki, sai shima ya zama kamar bawa a gare ki.

2 - Kada ki nisance shi, sai ya manta dake.

3 - Ki kiyaye masa hancinsa, jinsa, da ganinsa; kada ya shaki wani abu daga gareki sai
mai qamshi kada yaji wani abu daga bakinki sai mai daÉ—i kada yaga wani abu daga gareki sai mai kyau.

4 - Ki kiyaye masa lokacin Abincinsa da lokacin Baccinsa, domin yunwa tana hassala mutum, kuma gurbata masa bacci na fusata shi.

5 - Ki kiyaye masa Dukiyarsa, danginsa da gidansa, domin suna da matukar muhimmanci a gareshi.

6 - Ki guji yin farin ciki yayin da yake cikin bacin rai, kuma ki kiyayi yin bakin ciki, yayin da yake farin ciki.

7 - Ki girmama shi matuqa shima zai girmamaki matuqa, fiye da yadda kowa zai girmamaki.

8 - Ki sani cewa gwargwadon yadda kike amincewa da ra'ayinsa gwargwadon tausayawar da zai miki.

9 - Kada ki juya masa baya yayin da ya kusanto gareki.

10 - Ki sani yake 'yata baza ki sami yadda kike soba har sai
kin zabi yardarsa akan yardarki, kin fifita son ransa akan son ranki.

11 - Kada ki fiya naci ko fushi a lokacin da kike neman wani abu agareshi, sai ya kosa dake.

12 - Daga karshe don girman Allah ki yi hakuri ki zamo shimfida ga mijinki zai zamo rumfa a gareki.

ALLAH YASA SAURAN YAN'UWA MATA SUMA SUYI AMFANI DAWAN NAN NASIHA.

SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/DailyHadithss
Post a Comment (0)