CIYARWAR BARIN AZUMI

CIYARWAR BARIN AZUMI


Tambaya:---

 Malam ni inada mahaifi wadda shekarunsa yaja, Kuma Yana cikin yanayi na jinya tsawon wata 16. 
Bai samu damar yin azumin Ramadan da ta gabata ba. Wani malami ya cedani lallai zai ciyar Amma Bai min Karin bayani akan ciyarwar ba. Shin zan ciyar safe, Rana da yamma ne Koko zan iya deban abinci na tsawon ranakun Ramadan? 

Amsa

1) Babu sabanin fahimta a kan cewa tsofin da azumi ya ke wahalar da su, an mu su izinin dainawa, kuma za su ciyar da abinci. 

[AL-MUGNY; 4/396]

2) Idan tsoho ya kasa yin azumi kuma ba zai iya ciyarwa ba, to ciyarwan ya fadi daga kansa.

 [AL-MUGNY; 3/38, FATA'WA IBNI BAZ; 15/208]

3) Ciyarwan Mudun Nabiyyi biyu ne na hatsi, a na iya bayar da dafaffe mai iya Ä·osarwa sau Ä‘aya, a madadin kowace rana

 [AS-SUNANUL KUBRA; 4/235]


4) Abincin da a ka fi ci a gari ne a ke ciyarwa na rabin "Sa'i" kamar nauyin kilo 1 da rabi, don azumin kowace rana.

 [FATA'WA IBNI BAZ; 15/203]

5) Wani ba ya ciyarwar "Fidya" ta barin azumi a madadin wani sai da saninsa, domin ibada ce. Idan ya wakiltar to daidai ne.
 [LIQA'UL BA'BI; 150]


6) Babu laifi a ba mutum Ä‘aya ciyarwar rashin yin azumi, kuma daidai ne a rarrabata ga mabuÄ·ata.

 [AS-SUNANUL KUBRA LIL-BAYHAQY; 4/235]


7) Ba ya inganta a bayar da kuđi a madadin ciyarwar rashin yin azumi, a dalilin larura amintacciya ta Shari'a.

 [FATA'WA IBNI UTHAYMIN; 19/116]

Amsawa:-- Sheikh Abdurrazaq Yahya Haifan

Daga
MIFTAHUL ILMI

Zaku iya bibiyar mu a 

TELEGRAM MEDIA⇨https://t.me/miftahulilmii

TELEGRAM⇨https://t.me/Miftahulilm2​

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248

FACEBOOK⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Post a Comment (0)