Hukunce-Hukuncen Alwalar Mace Mai Yoyon Ruwa

Hukunce-Hukuncen Alwalar Mace Mai Yoyon Ruwa
:


TAMBAYA❓
:
Mace ce, ta yi Sallar Asuba da alwala alhali tana mai yoyon ruwa, ya halarta ta yi Sallar Walaha da wannan alwala?
:
AMSA👇
:
Mai irin wannan yoyon ruwa baya halatta tayi Sallar Walaha da alwalar Sallar Asuba don kuwa ba bayan Sallar Asuba take za’ayi ba, sai bayan fitowar rana don ita mai wannan yoyon ai kamar mai ciwon istihala ne. Tilasne ta yi alwala a kowane Sallah. Annabi (SAW) yace mai istihala tilas ne tayi alwala a kowane Sallah. Lokacin salloli kuma gashi:

1- Lokacin Sallar Azahar: Da zaran rana ta dan karkata da tsakiyar sama har zuwa La’asar.

2- Lokacin Sallar La’asar: Daga shigan SalIar La’asar har zuwa rana tayi fatsi-fatsi har zuwa faduwarta.
3- Sallar Magriba: Daga faduwar rana har zuwa bayan jan dake yamma (wato Shafak).

4- Sallar Isha’i: Daga bayan shafak, kuma har zuwa dare na karshe, har zuwa fitowar alfijir.

5- Sallar Asuba: Daga fitowar alfijir har zuwa dab da fitowar rana.

Allah ne mafi sani.


Post a Comment (0)