HAKKOKIN MAKWABTAKA
TAMBAYA❓
:
Assalamu Alaikum Warahmatallahi Wabarkatahu
Malam MENENE HAKKOKIN MAKWABTAKA A MUSULUNCI
Ngd
:
AMSA👇
:
Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu
wajibi ne kowane Musulmi ya san hakkokin makwabcinsa da suke kansa, tare da sanin ladaban zama da shi, idan ya san hakan, shi zai sa ya zauna da makwabtansa kamar yadda addini ya tsara.
Malamai sun bayyana makwabci cewa shi ne wanda in ka ƙidaya gidaje arbain daga jikin gidanka hagu da dama gaba da baya.
A tsarin Musulunci makwabta sun kasu zuwa kashi uku, kowanne da irin hakkokin da ke kansa, akwai mai hakki ɗaya da mai hakkoki biyu da kuma mai hakkoki uku.
1.Makwabci Musulmi, makusanci (Dan'uwa): Shi wannan yana da hakkoki uku, hakkin Musulunci ga hakkin makwabtaka, ga kuma hakkin 'yanuwantaka, wanda yake tsan-tsan ya ga ya dauke dukkan waɗannan hakkoki.
2. Makwabci Musulmi: shi wannan yana da hakkoki biyu ne kawai, wato hakkin makwabtaka, sai kuma hakkin Musulunci.
3. Makwabci wanda ba musulmi ba: shi ma nan yana da hakki ɗaya ne kawai wato hakkin makwabtaka.
Ubangiji mai girma da daukaka
ya fada cikin littafinSa mai girma, cikin suratul Nisa’i aya ta 36 cewa: “ KU BAUTATAMAN KARKUYI SHIRKA A GARE NI KUYI IHSANI GA IYAYE A KYAUTATA MUSU, DA MAKUSANTA, DA MARAYU, DA MABUKATA, DA MAKWABCI NA KUSA. ” hai izuwa karshin ayar.
Ayoyi da hadisai sun karfafa hakkin makwabci a kan makwabcinsa. Jibrilu (AS) bai gushe ba yana yi wa Annabi Muhammad ﷺ wasiyya a kan makwabci har sai da ﷺ ya yi tsammanin makwabci zai yi tarayya da makwabicnsa a cikin gado. Don haka babu mai munana wa makwabci ya cutar da shi face la’imi marar son alheri kuma abin kyama. Mai aikata dukan fasadi a bayan kasa.
Manzon Allah ﷺ yana cewa: “Wallahi bai yi imani ba! Wallahi bai yi imani ba! Wallahi bai yi imani ba! Aka ce, “Ya Manzon Allah! Hakika wannan kuwa ya tabe kuma ya yi asara, wane ne shi?” Ya ce: “Wanda makwabcinsa bai kubuta daga bawa’ikahu ba. Suka ce: “Mene ne bawa’ikahu?” Ya ce: “Sharrinsa.”
Har ila yau, Manzon Allah ﷺ ya ce: “Wanda ya kasance yayi imani da Allah da Ranar Lahira, to, ya girmama makwabcinsa, kuma wanda ya kasance ya yi imani da Allah da Ranar Lahira, to, ya girmama bakonsa, kuma wanda ya kasance yayi imani da Allah da Ranar Lahira, to ya fadi alheri ko ya yi shiru.” Kuma Manzon Allah ﷺ ya ce: “Mumini, shi ne wanda mutane suka aminta da shi. Musulmi kuma shi ne wanda Musulmi suka kubuta daga harshensa da hannunsa, mai hijira kuma shi ne wanda ya kauracewa mugun abu. Na rantse da Wanda raina yake hannunSa, wanda makwabcinsa bai kubuta daga sharrinsa ba, ba zai shiga Aljanna ba!”
Idan muka yi duba ga wannan Aya da waɗannan Hadisai za mu fahimci girman kyautatawa makwabci da girmama shi, domin girmama shi ma yana nuna cewa mutum ya bayar da gaskiya da Allah da ranar Lahira.
Abin kunya ne gare ka ya kai Musulmi! A ce ka kwana a koshe, amma makwabcinka ya kwana da yunwa! Abin kunya ne gare ka a ce ka yi sababbin tufafi amma ka yi rowar tsofaffin tufafinka ga makwabtanka marasa tufa! Kuma abin kunya ne gare ka a ce kana jin dadi da dadadan abinci da abin sha, amma makwabtanka suna neman kasusuwa da sauran abinci, alhali kana sane da fadin Manzon Allah (SAW): “Kada makwabciya ta raina abin da za ta ba makwabciyarta ko da kashin hakarkarin akuya ne kuwa.” Kuma ya ce da Abu Zarri (RA): “Ya Abu Zarri idan kana dafa nama ka yawaita ruwan (romo) don ka ba makwabtanka.”
Ya kai Musulmi! Lallai daga cikin hakkokin makwabci a kanka akwai cewa, ka yi masa sallama idan ka hadu da shi, kuma ka je gaida shi idan ba ya da lafiya, kuma ka raka gawarsa idan ya rasu, kuma ka kasance uba ga ’yan’yansa bayan rasuwarsa kamar yadda shi ya kasance musu a rayuwarsa. Ka tsaya a gefensa (tare da shi) a cikin kunci da yalwa da tsanani da wadata. Wata maganar hikima na cewa: “Wanda amfanar da ’yan uwansa ta kubuce masa, kada ya yarda amfanar da makwabcinsa ta kubuce masa!”
Kuma Manzon Allah ﷺ ya ce: “Mafi alherin aboki a wurin Allah Madaukaki, shi ne wanda ya fi alheri ga abokinsa, kuma mafi alherin makwabci a wurin Allah Madaukaki shi ne wanda ya fi yin alheri ga makwabcinsa.”
Haram ne a kanka ya kai Musulmi! Ka rika leka gidan makwabcinka alhali bai sani ba, ko ka ha’ince shi game da iyalinsa. Duk wanda ya leka gidan makwabcinsa ba tare da izininsa ba, Allah zai cika idonsa da wutar Jahannama. Kuma haram ne a gare ka rika kashe kunne domin ka ji abin da yake fada a cikin gidansa ka zama kamar mai leken asiri da maganarsa da aikinsa ba za su kubuta daga gare ka ba.
Kuma idan ba za ka iya kyautata wa makwabcinka da dadada masa ba, to ka kame daga cutar da shi, kada ka cutar da shi koda da gaisuwa don ya samu ya huta a cikin gidansa. Idan ya kira ka, ka amsa masa, idan ya nemi shawararka ka ba shi shawara tagari, idan aka zalunce shi ka taimaka masa, idan shi yake zaluncin ka hana shi. Idan ya kyautata ka gode masa, idan ya munana ka yi masa afuwa, idan ya aikata fasadi kada ka karfafa shi a kai, domin da yawa makwabci zai rike wuyan makwabcinsa a Ranar kiyama ya ce: “Ya Ubangijina! Lallai ne wannan ya rufe min kofarsa, ya ki yi min nasiha, ya gan ni ina aikata sharri bai hana ni ba.” Wani mutum ya ce, “Ya Manzon Allah! Lallai ana ambaton yawan Sallar wance da azuminta, sai dai tana cutar da makwabcinta.” Sai ya ce: “Tana cikin wuta!” Sai ya ce: “Ya Manzon Allah! Lallai wance ana cewa tana da karancin Sallah da azumi, amma tana yawan sadaka… kuma ba ta cutar da makwabtanta.” Sai (SAW) ya ce: “Tana cikin Aljanna.”
Manzon Allah (SAW) ya ce: “Abubuwa hudu suna daga cikin sa’ada: mace tagari da gida yalwatacce da makwabci nagari da abin hawa mai lafiya. Kuma abubuwa hudu suna cikin shakawa(tabewa da rashin sa’a): mugun makwabci da muguwar mace da mugun abin hawa da kuntataccen gida.”
Yana daga cikin hakkokin makwabtaka a kyautata masa ta kowanne hali, kamar aika masa da abin da ka dafa, bashi shawarwari da za su amfane shi, a kansa ko iyalansa, ko 'ya'yansa, tsawatarwa 'ya'yansa a kan abinda aka ga zai cuce su, domin kyautatawa makwabci yana kai mutum zuwa Aljanna.
"wani mutum ya je wajen Manzon_Allah ﷺ yace:"Ya Ma'aikin Allah shiryar da ni a bisa wani aiki, idan na tabbata a kansa zan shiga Aljanna, sai yace: "Ya Ma'aikin Allah ta ya ya zan san ni mai kyautatawa ne? Sai ya ce: Tambayi makwabtanka idan suka ce kai mai kayutatawa ne to shi ne, amma idan suka ce kai ba mai kayuatatawa ba ne, to ba shi ba ne".
Wannan Hadisi yana nuna mana cewa idan mutum yana son ya san matsayinsa, to ya tambayi makotansa sune shaidarsa a kan shi mai kyautatawa ne ko a'a, don haka wajibi ne mu zamo masu kyautata musu don mu samu kyakkyawar shaidar cewa mu masu kyautatawa ne, don in muka zamo masu kyautatawa, to mun kama hanyar zuwa Aljanna.
Ibn Umar ya kasance yana da makwabci Bayahude, idan ya yanka akuya sai ya ce: ku kai wa makwabcina Bayahude wannan (Abu Dawud da Tirmizi).
Har ila yau, kiyaye mutuncinsa(Makwabci) dana iyalinsa da dukiyarsa suna daga cikin kyautatawa, domin Annabi ﷺ yace: "Mutum ya yi zina da mataye goma shi ya fi sauki a gare shi da yin zina da matar makwabcinsa, mutum ya yi sata a gidaje goma shi ya fi sauki a gare shi da yayi sata a gidan makwabcinsa" (Ahmad).
Ya zo cikin sunani Abu Dawud daga Aba Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce: "wani mutum ya zo wajen Ma'aikin Allah ya kawo karar makwabcinsa, sai ya ce da shi, ka je ka yi hakuri, sai ya sake zuwa na biyu ko na uku, sai Manzon Alla ya ce: jeka ka debo kayanka ka zuba a kan hanya, sai ya je ya sanya duk lokacin da mutane suka zo wucewa sai suka tambaye shi bisa halin da yake ciki, sai ya basu labarin irin cutar da makwabcinsa yake yi masa Sai suka rinka la'antar makwabcin, sai makwabcin ya zo gare shi ya ce: ya dan uwana mayar da kayanka gidanka ba zaka kara ganin wani abu na rashin kyautatawa ba daga
gareni har abada".
Ya bayin Allah! “Lallai ne Allah Yana umarni da adalci da kyautatawa da ba ma’abucin zumunta (hakkinsa), kuma Yana hani daga alfasha da abin ki da zalunci, Yana yi muku wa’azi tsammaninku za ku yi tunani.” Don haka ku tuna Allah Mai girma da daukaka, sai Ya tuna da ku, kuma ku gode maSa a bisa ni’imominSa, sai Ya kara muku. Kuma ambaton Allah ne mafi girma. Kuma Allah Yana sanin abin da kuke aikatawa.
Wallahu A'alamu
Yaku Yan'uwa masu Albarka ku taya mu yaɗa wannan karatu/sako zaku samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.