Hukuncin Zagin Sahabban Annabi (ﷺ)



Ramadaniyyat 1442 [30]

Dr. Muhd Sani Umar (Hafizahullah)

Hukuncin Zagin Sahabban Annabi (ﷺ)
____________________________________

1. Zagin sahabban Manzon Allah (ﷺ) haramun ne, kamar yadda dalilai masu yawa a cikin littafin Allah da sunna suka tabbatar. Domin kuwa Allah ya harmta yi da mutane. Mafi karancin laifin mai zagin su ya shiga karshin ayar da ta haramta cin naman mumini.
2. Allah ya tabbatar da cewa, duk wadanda suke cutar da muminai maza da mata ba laifin zaune ba na tsaye, to su sani cewa, lalle sun daukar wa kansu laifin kage da kuma zunubi bayyananne. [Ahzab, aya ta 58].
3. Sahabbai su ne kan gaba a tawagar muminai, domin duk wata aya mai cewa, "Ya ku wadanda suka yi imani" to su ne farkon wadanda suka amasa wannan kiran. Ba kuma su yi wani laifin da har zai sa ya rika cutar da su ba, domin kuwa Allah ya riga ya yarda da su [Suratut Tauba, aya ta 100]. 
4. Sifar yarda ta Allah, siffa ce kadimiya. Allah ba zai taba yarda da wanda ya riga ya san ba zai cika da sharadin samun yardarsa ba. Don haka duk wanda Allah ya yarda da shi, to ba zai taba yin hushi da shi ba har abada.
5. Malamai duka sun hadu a kan cewa, duk wanda ya tuhumi Nana A'isha (Allah ya yarda da ita) da laifin da Allah ya wanke ta daga gare shi, to wannan kai tsaye ya kafurta, domin kuwa ya karyata Alkur'ani a fili.
6. Hakanan duk wanda ya yi wa daya daga cikin matan Annabi (ﷺ) kazafi, shi ma ya kafurta, domin yin haka cin mutunci ne ga Manzon Allah (ﷺ).
7. Duk kuma wanda ya zagi wani daga cikin sahabban Annabi (ﷺ) to dole ne alkali ya yi masa horo mai tsanani, ya kuma tsare shi har sai ya tuba, ko ya yi ta zama a tsare har zuwa mutuwarsa. Wannan ita ce mashahuriyar magana a mazhabar Imamu Malik (Rahimahullah).

Post a Comment (0)