KAR KA DAMU DA MASU HASSADA
Kar ka damu da hassadar masu hassada. Wannan ba zata Cuceka ba, mutukar ka rike Allah. Shi Allah din zai isar maka.
Daga lokacin da ka fahimci cewa wane ba ya Qaunarka, ko kuma wane yana yi maka hassada, to kar ka Qishi. Kar ka rama abinda yake yi ma.
Ka sani cewa kyautatawa zuwa ga masu yi maka hassada, yana Qara maka daukakar daraja ne awajen Allah. Sannan kuma yin hakan zai zama garkuwa gareka daga sharrinsu.
Ita hassada guba ce wacce take saurin hallakar da masu yinta, tun kafin ta shafi wanda akayi dominsa.
Don haka idan ka kyale Mahassada da halinsu, sharrinsu ma ya ishesu bala'i.
Shi yasa Allah ya umurci Annabinsa (saww) cewa ya nemi tsari daga sharrin Mai Hassada yayin da yake hassadarsa.
Ya Allah ka kiyayemu daga sharrin mahassada da matsafa da miyagu albarkacin hasken Alqur'aninka. Aaameeen.
DAGA ZAUREN FIQHU