KAYIWA KANKA HISABI KAFIN MUTUWA TA SAMEKA

KAYIWA KANKA HISABI KAFIN MUTUWA TA SAMEKA


Ibn Qayyim Allah yayi masa Rahama yana cewa;-
●Kafara yiwa kanka hisabi akan;Inganta Imaninka da
Aqeedarka,idan ka sami tawaya acikinta sai kayi kokarin gyara Imaninka da aqeedanka ta zama irin ta Manzon Allah 
s .a.w da sahabai

●Sannan sai kayi wa kanka Hisabi akan Farillar da Allah ya
dora maka,idan a kwai naqasa acikinsu sai ka gyarau, ko dai ta hanyar ramawa ko ta hanyar cikawa da kyautatawa.

●Sannan hisabi akan abubuwan da Allah yayi hani akansu.
Idan har ka ketara wani daga cikinsu sai kayiwa kanka
Hisabi, Ta hanyar tuba da Istighfari da yawaita kyawawan
aiyuka sai su goge wannan laifin

●Sannan kayiwa kanka Hisabi akan gafala da sakaci,idan
ka sami gafala da sakaci akan wadansu halaye masu
kyau,to sai ka gyara su ta hanyar ambaton Allah da komawa zuwa ga Allah.

●Sannan Hisabi akan abinda Hashenka yake furtawa,ko
inda kafarka take takawa zuwa wani waje,da abinda
Hannunka yake tabawa,ko kunnanka suke sauraro da
abinda idanuwanka suke kallo,dukkan abin kiyayewane
domin abin tambayaye a gobe alqiyma,kada ka barsu su kaika zuwa ga halaka,sai kayi masu hisabi ta hanyar kada
su fadi komai sai Alkhairi kuma kada su aikata komai sai
Alkhairi.

●Ya kamata mu sani lallai dukkan motsin da mukayi da
maganar da muka faɗa da abinda muka taɓa da inda
muka taka zuwa wani waje da abinda muka saurara da kunnuwan mu dukkan su abin tambayane agobe alqiyama.

Tambaya ta farko da zakayiwa kanka shine
Shi dukkan bauta da nakeyi inayine dan Allah shi kadai
dan neman yardar Allah???

Shin Ibadata da wa nake koyi??shin irin ta Manzon Allah s.a.w ce??

Allah yana cewa;
*﴿ ﻓﻮﺭﺑﻚ ﻟﻨﺴﺄﻟﻨﻬﻢ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ ﻋﻤﺎ ﻛﺎﻧﻮﺍ ﻳﻌﻤﻠﻮ﴾ .
@ ﺍﻟﺤﺠﺮ : ٩٢ - ٩٣
*﴿ ﻓﻠﻨﺴﺌﻠﻦ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺃﺭﺳﻞ ﺇﻟﻴﻬﻢ ﻭﻟﻨﺴﺌﻠﻦ ﺍﻟﻤﺮﺳﻠﻴﻦ ﻓﻠﻨﻘﺼﻦ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﺑﻌﻠﻢ ﻭﻣﺎ
ﻛﻨﺎ ﻏﺎﺋﺒﻴﻦ﴾ . @ ﺍﻷﻋﺮﺍﻑ : ٦ -٧
*﴿ ﻟﻴﺴﺄﻝ ﺍﻟﺼﺎﺩﻗﻴﻦ ﻋﻦ ﺻﺪﻗﻬﻢ﴾
@ﺍﻷﺣﺰﺍﺏ : ٨
Idan har Allah zai tambayi masu yawan gaskiya akan
gaskiyarsu kuma ayi masu Hisabi,me kake tsammanin mai karyata da abinda suka aikata na karyarsu.
@ ﺇﻏﺎﺛﺔ ﺍﻟﻠﻬﻔﺎﻥ ‏( ٨٣/١ ).
 ﻻﺇﻟﻪ ﺇﻻﺍﻟﻠﻪ
 ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﺭﺯﻗﻨﺎ ﺍﻟﺤﻴﺎﺀ ﻣﻨﻚ ﺳﺮﺍً ﻭﻋﻼﻧﻴﺔ ﻭ ﻭﻓﻘﻨﺎ ﺇﻟﻰ ﺍﻹﺧﻼﺹ ... ﺁﻣﻴﻦ


Post a Comment (0)