KU KAWO GYARA BA ƁARNA BA

KU KAWO GYARA BA 6ARNA BA


 Ash-Shaykh Saalih Al-Fawzaan, Allah ya kiyaye shi, yace:

 "Akwai wani gargadi mai tsanani da yazo ga wadanda suke 6ata alakar dake tsakanin mata da mijinta, su riqa zugata tana sa6a masa. Yazo a cikin ruwaya cewa: "La'ananne ne wanda ya juyar da mace daga mijinta." 
 [Al-Hakim ya kawo acikin Mustadrak ɗinsa] 

Wannan yana nufin wandanda suke zama dalilin munanan dabi'u/mu'amala da take yi masa da taurin kai a gare shi. Don haka ya zama wajibi ga dangin matar (ko kawaye ko duk wasu masu zugatan) da su himmatu kadai wajen kawo gyara a tsakanin ma'auratan, domin hakan yana da amfani a gare ta da su” (hakan shi zai kubutar dasu daga fadawa la'anar da ta gabata, itama ta tsira daga fushin Allah da mummunan tanadi a lahira ga wadda ke cutar da mijinta)
 
📕 [Al-Muntaqa min Fatāwá 55/16]

#Zaurenfisabilillah

Telegram:
https://t.me/Fisabilillaaah

Instagram:
https://www.instagram.com/zaurenfisabilillah/
Post a Comment (0)